Ziyararmu Amurka tubarkallah – Al-Makura

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura yana cikin gwamnonin da suka raka Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ziyarar da ya kai Amurka a kwanakin baya. A tattaunawarsu da wakilinmu Gwamna Al-Makura ya ce sun yi nasara a wannan ziyara da suka kai Amurka: Aminiya: Me za ka ce game da nasara ko akasin haka a […]

Ziyararmu Amurka tubarkallah – Al-Makura
Ziyararmu Amurka tubarkallah – Al-Makura

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura yana cikin gwamnonin da suka raka Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ziyarar da ya kai Amurka a kwanakin baya. A tattaunawarsu da wakilinmu Gwamna Al-Makura ya ce sun yi nasara a wannan ziyara da suka kai Amurka:

Aminiya: Me za ka ce game da nasara ko akasin haka a ziyarar da kuka kawo nan Amurka?
Al-Makura: Da farko dai zan bayyana farin cikina kwarai-kwarai na nasarar da wannan ziyara da aka samu musamman na ganin yadda gwamnatin Amurka da shugabannin Amurka da manyan ’yan kasuwa da manyan hukumomi suka nuna wa Shugaban kasarmu Muhammadu Buhari. Wannan irin martabawa da kauna da mutunci da suka nuna mana, ya nuna cewa ashe Amurka tana sha’awar samun kyakkyawar hadin kai da mu Najeriya, sai dai rashin samun mutumin da yake da akida da manufa mai ma’ana da dace da manufofin da suke so, samun mutum irin Buhari ne ya kawo mana kwarjini da martabar da suka ba shugabanmu da muka zo wannan ziyara.
Aminiya: Wace tattaunawa kuka samu yi da ’yan kasuwar Amurka domin zuwa jihohinku su zuba hannun jari?
Al-Makura: Wato babbar fa’ida ce samun zuwa cikin tawagar Mai girma Shugaban kasa, zuwa wannan kasa ta Amurka wadda tana daya daga cikin kasashe masu karimci da girma da martaba a idon duniya, ba shakka samun wannan zuwa ziyara ta bude mana ido da karfin gwiwa kan irin tunani da maganganun da muka yi da jami’an Amurka wadanda suka shafi muhimmam abubuwa musamman kan sha’anin tsaro, sun nuna tausayawarsu kwarai da gaske kan lalurar da ta samu kasarmu, kuma a shirye suke su ba da  gagarumar gudunmawa da taimako da goyon baya domin a samu magance wannan lalura. Batu na biyu kuma shi ne sun yaba wa Shugaba Buhari kan irin akida da kyakkyawar niyyar da yake da ita wajen tallafa wa ’yan Najeriya su fita daga kangin da suke ciki musamman na cin hanci da rashawa da munanan ayyukan da suka mayar da kasarmu baya. Sun karbe shi hannu bibbiyu ganin cewa ya fito ne da kyakkyawar niyya da akida wanda tuntuni ake ta fatar Najeriya ta samu. To wannan ya kara buda mana dama wajen tattaunawa game da maganar cinikayya da gudunmawar da za su ba da don ganin sun kara wa Najeriya taimako a magance abubuwa da dama da suka mayar da kasar baya, musamman abin da zai bunkasa arzikin kasarmu Najeriya da samar da ababen jin dadin rayuwa da suka hada da asibitoci da sauransu.
Aminiya: Wane irin mutum ne kai ka fahinci Shugaba Muhammadu Buhari?
Al-Makura: Buhari mutum wanda Allah Ya taimaki Najeriya da ta same shi, domin shi ne maganin matsalar Najeriya, saboda mutum ne mai tausayi da zimmar ganin talaka ya samu abin da ya kamata a ce ya samu kuma mutum ne mai son a bi doka da oda. Najeriya ta dade tana neman irin wannan mutum sai yanzu ta yi sa’a ta samu. Don haka ya zame mana wajibi mu ’yan Najeriya wajibi ne mu ba shi goyon bayan da ya dace. Yana cikin sahun shugabannin da ake jin sunayensu a duniya saboda irin akidarsa, kamar su Shugaba Obama, su Dabid Cameroun da dai fitattun shugabannin duniya, don haka Najeriya ta yi sa’a.
Aminiya: To, a karshe me za ka ce game da zaben da ya kawo shi kan karagar mulki?
Al-Makura: Wannan zabe shi ne ba-zata, domin ba a taba ganin na waje ya kada na ciki ba, a zaben Shugaban kasa sai wannan. Wannan shi ne abin da ya faru a Najeriya domin zabe ne sahihi wanda duniya ta amince da shi, su ma wadanda aka kayar sun san gaskiya ba ta canzuwa, domin zabe ne wanda ba a taba yin irinsa ba a Najeriya. Yana cikin abin da ya sa ya samu karbuwa a kasa irin wannan, shi ya sa hatta makiyansa ma suka amince. Kuma wurin da aka sauke shi a Amurka ba wuri ne da ake sauke kowa da kowa sai idan ka kai ka kawo a wajenta, mukan zuwanmu tubarkallah.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi