Zlata: Macen da ta shahara wajen lankwasa sassan jikinta

Julia Günthel, wadda aka fi sani da Zlata, wata matashiya ce ’yar shekara 28, haifaffiyar kasar Rasha, ta shahara a duniya saboda iya lauya sassan jikinta yadda tag a dama. Wannan matashiya ’yar kasar Rasha, ta shiga cikin kundin duniya, saboda gwanancewarta wajen lankwasa jikinta, domin ba a samu wanda ya kamota ba.Ta fada da […]

Zlata: Macen da ta shahara wajen lankwasa sassan jikinta
Zlata: Macen da ta shahara wajen lankwasa sassan jikinta

Julia Günthel, wadda aka fi sani da Zlata, wata matashiya ce ’yar shekara 28, haifaffiyar kasar Rasha, ta shahara a duniya saboda iya lauya sassan jikinta yadda tag a dama.

Wannan matashiya ’yar kasar Rasha, ta shiga cikin kundin duniya, saboda gwanancewarta wajen lankwasa jikinta, domin ba a samu wanda ya kamota ba.
Ta fada da bakinta, cewa: Yin wadannan lankwashe-lankwashe ina yinsu ne kawai saboda na saba. Kodayake a wasu lokutan na kan ji babu dadi, musamman idan an sanya ni in dade, domin a dauki hotuna. Kafafen yada labarai na duniya sun sha baje hotunanta, amma jaridar dailymail ce ta fara yin cikakken labara a kanta, tun a shekarar 2013.