Zubar da jini: A sake lale!
A wannan mako an kashe kusan mutum 100 a jihohi biyu kacal a nan Arewa. Mutum 51 ’yan bindigar da ake zargi Fulani ne masu garkuwa da mutane suna amsar kudin fansa suka kashe a wasu kauyukan Jihar Kaduna, yayin da sama da mutum 40 da ake zargin ’yan bindiga masu garkuwa da mutane ne […]
A wannan mako an kashe kusan mutum 100 a jihohi biyu kacal a nan Arewa. Mutum 51 ’yan bindigar da ake zargi Fulani ne masu garkuwa da mutane suna amsar kudin fansa suka kashe a wasu kauyukan Jihar Kaduna, yayin da sama da mutum 40 da ake zargin ’yan bindiga masu garkuwa da mutane ne wata tsohuwa mai shekara 70 ta jagoranci kashe su a Jihar Neja.
Zubar da irin wannan jini ko a fagen yaki ne babban abin tashin hankali ne balle a ce auka wa mutane ake yi haka siddan ana kashe su. Ko kuma an kashe su ne bisa zargin suna da hannu a wani laifi da kotu ba ta tabbatar ba.
Su dai mutum 51 da aka kashe an hallaka su ne a kauyukan Kerawa da Zariyawa da Marina da Rago da Hashimawa da Gidan Musa Sa’idu da kuma Unguwar Barau da ke Karamar Hukumar Igabi da Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Kamar yadda rahotanni suka nuna makasan sun yi jijjifi ne wa mutanen kauyukan da misalin karfe 6 na safe inda suka kashe na kashewa sannan suka banka wa gidajensu wuta tare da sace kayan abincinsu.
Kansilan Kerawa Malam Dayyabu Kerawa wanda ya tabbatar da kai harin ga wakilan Aminiya a karon farko ya tabbatar da kashe mutum 51 wadanda aka kammala jana’izarsu da misalin karfe 4 na yamma.
Wannan kisan gilla na zuwa ne bayan kashe mutum 21 a kauyen Bakali da ke Gundumar Fatika a Karamar Giwa a ranar 12 ga watan jiya. A wacan ta’asa ’yan bindigar sun kashe mutum 16 iyalan gida daya sannan suka kone gidansu kuma suka kashe wadansu mutum biyar ciki har da jami’an tsaro na sa-kai (JTF). Washegari haka kuma wadansu ’yan bindigar suka bude wuta a Kasuwar Maro a Karamar Hukumar Kajuru inda suka kashe mutum bakwai a yammacin ranar, tare da raunata wadansu da dama.
A can Jihar Neja kuma maharba a karkashin jagorancin wata mata mai shekara 70 ne aka ce sun kashe ’yan bindigar da suka kai 40 a Zuguruma da ke Karamar Hukumar Mashegu da ke jihar a artabun da suka yi cikin minti 30.
An ce an kuma kama kwamandan ’yan bindigar da wadansu mutum uku ne suka shiga gari sayen katin waya da sauran kayayyakin bukatun rayuwa ga jama’arsu inda aka mika su ga hedkwatar ’yan sandan jihar.
Wani mazaunin kauyen mai suna Malam Alhassan, ya ce lokacin da mafarautan suka shiga dajin matar ta umarci maharban su yi harbi a sama don jawo hankalin ’yan bindigar.
“Kuma ’yan bindigar na jin karar bindiga sai suka mayar da martani har sai da harsasansu suka kare, sai maharban suka auka musu inda suka kashe mutum 40 daga cikinsu,” inji shi.
Ya ce babu wanda aka kashe daga bangaren maharban.
Tuni Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya ziyarci wasu daga cikin kauyukan da aka kai wa hare-haren a kananan hukumomin Igabi da Giwa inda ya sha alwashin murkushe ’yan bindigar.
Bayanai dai sun ce maharan sun kai hare-haren ne don huce fushi a kan mutane kauyen wadanda suke zargi da ba hukumomin tsaro bayanan da suka sa aka kai musu farmaki a kwanakin baya.
A gaskiya yadda ake zubar da jini a kasar nan kama daga kashe-kashen da ’yan ta’addan Boko Haram suke yi zuwa kashe-kashen da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane ko satar shanu da sauran barayi ke yi babban abin takaici ne.
Babu wani addinin da ya amince da zubar da jini irin yadda ake yi a Najeriya. Babu wani lafiyayyen hankali da zai amince da irin wannan zubar da jini da ake yi a kasar nan. Ko kasashen da ake yaki irin su Iraki da Libya da Siriya ba su kai Najeriya zubar da jini ba.
Ban san addinin da masu wadannan kashe-kashe suke bi ba, amma na hakkakke addinin Musulunci da addinin Kirista da addinin garjiya da su kadai muke da su a Najeriya ba su yarda da daukar ran dan Adam haka siddan ba. Kuma addinan ba su yarda idan wani ya kashe maka dan uwa ka kashe shi ba, a’a sai dai ka kai batun ga hukumar ta yi hukuncin da ya dace a kai.
Don haka abubuwan da suke faruwa a yanzu sai ka rasa wane irin majanunanci ne muka samu kanmu a ciki da ake zubar da jini ba kakkautawa haka. Shin jahilci ne ke kawo haka ko kuwa shaye-shaye da tabarbarewar tarbiyya da neman tara abin duniya dare daya kuma ido rufe?
Ko ma me ke kawo haka, ina ganin ya kamata hukumomin Najeriya su canja salo a yakin da suke yi da miyagun cikinmu, wuta ba ta kashe wuta kamar yadda wadansu suke tunani. Idan wuta ta kamata ruwa ne yake kashe ta, don haka hukumomin tsaro su zauna su yi tunani ta ina matsalar take? Shin akwai bara-gurbi ne a jami’an tsaro da suke cin gajiyar wadannan miyagun ayyuka ko kuwa me yake faruwa?
Kamar yadda muka wuta ba ta kashe wuta, lokaci ya yi da jami’an tsaro da hukumomin tsaro za su daina dogaro da tura jami’an tsaro dauke da miyagun makamai a kan tituna kadai, a koma ga tsarin samar da bayanan sirri na miyagun da suke cikin jama’a suke aikata ta’asa ko suke taimakawa a aikata ta’asa don a gano inda suke zaune a kama su a hukunta su.
Bayanan da mutanen kauyukan kananan hukumomin Igabi da Giwa da aka kai wa hari suka yi sun nuna cewa maharan suna zarginsu ne da ba hukumomin tsaro bayanan da suka taimaka aka kai musu hari a dajin Birnin Gwari a kwanakin baya.
Wannan yana nufin lallai ne a kara samar da jami’an tsaro na sirri masu amana da za su yi wannan babban aiki na gano maboyar miyagu ana magance ta’asarsu. Amma babban abin takaici sai ringima-ringimar shingaye binciken ababen hawa na soji da ’yan sanda muke girkewa sai ka ce ’yan bindigar da ’yan ta’adda suna shawagi a kan wadancan titunan ne.
Abu na biyu wajibi ne hukumomin tsaro wato ’yan sanda da jami’an tsaron kasa (SSS ko DSS) da jami’an leken asiri da sojoji da duk wanda harkar tsaro ta shafa su tsaya su yi aiki tare. Su kawar da jiji da kan da suke nunawa na na fi iya aiki ko in ba ni ba, kowa ya rasa.
Ga shugabannin wadannan hukumomi tun daga matakan gundumomi zuwa kananan hukumomi zuwa jihohi zuwa kasa, wajibi ne su nuna da gaske suke yi a harkar tsaro. Abin takaici ne da ba mu jin ana ladabtar da shugabannin tsaron da suka nuna gazawa tun daga unguwanni zuwa gundumomi zuwa kananan hukumomi zuwa jihohi balle matakin kasa.
Ya kamata Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Malam Mohammed Adamu ya ba wa kowane kwamishinansa umarnin cewa zai hukunta shi idan aka samu gazawa iri kaza, shi ma ya hukunta DPO idan aka samu gazawa iri kaza a karkashinsa haka lamarin ya tafi har unguwa.
A can kololuwa kuma Shugaban Kasa ya kamata ya shafa wa fuskarsa tokay a nuna ba sani ba sabo ga shugabannin tsaro na kasar nan. Idan ana zargin wadansu ne suke yi musu zagon kasa saboda suna hangen kujerar da suke kai, me zai hana a zakulo masu zagon kasan a hukunta su? Ida nana zargin akwai masu zagon kasa daga ciki ko wajen jami’an tsaron me zai hana a yi amfani da jami’an tsaro na sirri wajen samo gamsassun hujjojin da za a iya gurfanar da su a gaban kotu a hukunta su?
Ya kamata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya daina karbar kowane uzuri kan gazawar shugabannin tsaron, ya ba su wani kayyadajjen lokaci na gano masu hannu a kashe-kashen nan, idan kuma suka gaza a sauke su. Ya ba su kayayyaddajen lokaci su kawo karshen Boko Haram idan suka gaza a sauke su a nada wadansu, su ma a ba su wani lokaci a nuna musu ga aikin da ake bukata in sun gaza ba ma za a tabbatar da su kan kujerar ba, balle su ci gaba.
An yi haka lokacin tsohon Shugaban Kasa na soja Janar Ibrahim Babangida, bayan da wani hatsabibin dan fashi Lawrence Anini ya addabi tsohuwar Jihar Bendel. Bayanai sun nuna cewa Janar Babangida ya cire Shugaban ’Yan sandan Najeriya na lokacin ne ya nada Alhaji Gambo Jimeta ya ba shi wani lokaci cewa ya kamo wannan dan fashi ko shi ma a yi waje da shi. Kuma cikin kwanaki kadan sai ga Anini a hannu, inda aka gano babban jami’in yaki da ’yan fashi na Rundunar ’Yan sandan Jihar George Iyamu ne yake daure masa gindin wannan ta’asa da yake yi. Don haka a yi amfani da jami’an tsaro na sirri don gano bakin zaren kowa ya huta.