Zuciyar mutum (2)

A makon da ya gabata, mun soma koyarwar a kan zuciyar mutum. Mun gane cewa lokacin da Allah Ya halicci mutum, zuciyarsa babu mugunta ko kazanta ko kadan a cikinta. Tun lokacin da mutum ya ki yin biyayya ga umarnin da Ubangiji Allah Ya ba shi, ya bi muryar Shaidan maimakon ya bi muryar Allah, […]

Zuciyar mutum (2)

A makon da ya gabata, mun soma koyarwar a kan zuciyar mutum. Mun gane cewa lokacin da Allah Ya halicci mutum, zuciyarsa babu mugunta ko kazanta ko kadan a cikinta. Tun lokacin da mutum ya ki yin biyayya ga umarnin da Ubangiji Allah Ya ba shi, ya bi muryar Shaidan maimakon ya bi muryar Allah, zuciyar mutum ta gama dagulewa, “zuciya ta fi komai rikici, ciwuta gare ta kwarai irin ta fidda da zuciya: wa za ya san ta? Ni Ubangiji mai bimbinin zuciya ne, ina gwada ciki, domin in saka wa kowane mutum bisa ga ayyukansa, bisa ga ’ya’yan aikinsa.” (Irmiya:17 : 9 – 10 ). Rikicin zuciyar mutum ba yanzu ta soma ba, ta soma ne tun lokacin zunubi na farko da Adamu da Hauwa’u suka aikata.  

Mine ne zuciya?  

Domin wannan bincike, za mu so mu bayyana zuciya kamar haka: Zuciya: ita ce mazaunin tunanin mutum, Littafi Mai tsarki yana koya mana cewa, “Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da kake kiyayewa: Gama daga cikinta mafitar rai suke.” (Misalai: 4: 23 ). Yesu Almasihu, ya koya mana cewa, “Ya ce musu, Har ku ma kun rasa fahimi haka? Ba ku gane ba, iyakar abu daga waje wanda ya shiga cikin mutum, ba za ya ita kazantar da shi ba; gama ba ya shiga cikin zuciyatasa, amma cikin cikinsa, ya fita kuma cikin salga? Wannan ya fadi garin ya maida abinci duka halal. Ya ce kuma, Abin da ke fitowa daga cikin mutum, shi ke kazantar da mutum. Gama daga ciki, daga cikin zuciyar mutum, miyagun tunani ke fitowa, fasikanci da sata da kisan kai da zina da kwadayi da mugunta da ha’inci da mugun buri da maita da zage-zage da girman kai da wauta: dukan wadannan miyagun abubuwa daga ciki suke fitowa, suna kazantar da mutum.” (Markus: 7:18 – 23). Allah cikin ikonSa, bai halicci mutum da irin wannan hali ko tunani ba, amma wannan gado da muka yi daga wurin mutum na farko wato Adamu da matarsa Hauwa’u, dalilin da ya sa ke nan babu wani dan Adam da zai iya ya yi abin da zai gamshi Ubangiji Allah, ko ya faranta wa Allah zuciya in bai bi tsarin da Allah Ya shirya wa mutum ya jawo shi kusa da shi ba. Za mu yi kokari mu dubi wannan shiri na Allah domin mutum a gaba kadan.  Allah Yana so mu kaunace shi da dukan zuciyarmu. Ashe zuciya tana nan kamar wuri ne a cikin mutum inda za mu iya yi wa Allah Madaukakin Sarki sujada, mu bauta maSa, mu kuma nuna kaunarmu gare Shi. “Za ya zama kuwa, idan kun kasa kunne da aniya ga dokokiNa wadanda Nake dokatar ku da su yau, cewa, ku yi kaunar Ubangiji Allahnku, ku bauta maSa da dukan zuciyarku da dukan ranku.” (Kubawar Shari’a: 11 : 23 ). 

Kowace irin ibada da muke so mu yi, idan ba daga cikin zuciyarmu take ba, aikin banza ne kawai, mu sani cewa Allah ba zai ma kula da abin da muke yi ba balle mu samu albarkar bauta maSa. Lokacin da Allah Ya gaya wa Annabi Samuila ya je gidan Jesse domin ya kebe daya daga cikin ’ya’yansa ya zama Sarkin Isra’ila, maimakon Sarki Saul wanda Ubangiji Allah Ya ki domin rashin biyayyarsa da yaran suka zo, sai Samuila ya ga Eliab, da ya dube shi sai ya ce “Lallai shafaffe na Ubangiji yana gabansa….” Nan da nan Ubangiji Allah Ya ce masa “……Samuila, kada ka dubi fuskarsa, ko kuwa tsawon jikinsa: gama na ki shi: gama ganin Ubangiji ba kamar na mutum ba ne: gama mutum yana duban aini, amma Ubangiji yana duban zuciya.” (1Samuila: 16 : 7) Yayin da mutum zai iya rudin dan uwansa mutum ta wurin kwazon da yake nunawa a cikin aiki, ko na ibada, ko na ma’aikata, babu wanda ya isa ya rudi Allah domin a koyaushe, Ya san abin da cikin zuciyar kowa. Abin da ke da muhimmanci ga Allah shi ne yanayin zuciyar mutum; ko tana da tsarki ko kuwa cike take da mugunta. Allah ba Ya amfani da mutum mai kazantacciyar zuciya. 

Wace irin zuciya ne kake da ita a yau? Idan Ubangiji Ya leka cikin zuciyarka; mene ne zai gani? Zuciya cike da mugunta ko kuwa zuciya cike da alheri da nagarta?

Yadda zuciyar mutum ke aiki:

“Algus yana cikin zuciyar wadanda ke tsirar da mugunta: Amma farar zuciya tana ga masu shawarar salama.” (Misalai: 12 : 20). “Mai kiyayya yakan yi kinibibi da bakinsa, Amma rikici yake ajiyewa a zuciyatasa: Sa’adda yana magana mai dadi, kada ka ba shi gaskiya: Gama akwai abin kyama guda bakwai a cikin zuciyatasa: Koda kiyayyatasa tana rufe da algus, muguntassa za ta tonu a sarari gaban taron jama’a.” (Misalai: 26 : 24-26). 

Mutum yakan iya boye abin da ke cikin zuciyarsa; za ka ga kamar yana yi maka dariya amma abin da ke cikinsa sai Allah ne kadai Ya sani. A fuskarsa, za ka yi tsammanin aboki ne amma cikin zuciyassa wani abu daban za ka iske. “Zuciya ta fi komai rikici, ciwuta gare ta kwarai irin ta fidda zuciya: wa za ya san ta?’ (Irmiya:17 : 9). Maganar Allah ta ce, babu wanda ya san abin da ke tafe a zuciyar mutum, amma abin da muka sani shi ne, zuciyar mutum ta fi komai rikici, kada mu manta, Allah bai halici irin wannan zuciya mai rikici, mai mugunta, mai tunanin rudin mutum, mai cin amana daga farko ba; lokacin da Ubangiji Ya halici Adamu da Hauwa’u, zuciyassu tana da tsarki a gabanSa, har sai lokacin da suka ki bin umarnin Allah suka saurari muryar Shaidan. 

Wani irin shiri ne Allah Ya yi domin ya taimaki zuciyar mutum? 

A cikin Littafin Farawa 3: 6 – 7, mun gani cewa mutumin da Allah Ya halitta da matarsa sun yi rashin biyayya ga maganar Allah, “Sa’ad da macen ta lura itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itace kuma abin marmari ne domin bada hikima, sai ta diba ’ya’yansa, ta ci; ta kuma ba mijinta tare da ita, shi kuwa ya ci. Dukansu biyu kuwa idanunsu suka bude, suka waye kuma tsirara ne su; suka dundunke ganyayen baure suka yi wa kansu mukuru.”

Ina so mu lura da wadansu abubuwa kadan daga wannan wurin kafin mu shiga binciken da muke so mu yi a kan irin shirin da Allah Yake da shi domin mutum; abu na farko dai shi ne: Allah Ya yi mutum da suturarsa har sai lokacin da ya yi zunubi kafin ya rasa wannan sutura. Zunubi yakan maida mutum ya zama tsirara a gaban Allah, abin kunya da kyama kuma. Maganar Allah ta koya mana cewa “Da shi ke dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” (Romawa 3 : 23). Allah Ya suturta mutum da darajarsa ne daga farko, abin da muka rabu da shi ke nan lokacin da Adamu da Hauwa’u suka aikata zunubin da suka yi. Suna gane cewa sun rabu da wannan daraja, sai suka soma neman abin da za su rufe tsiraicinsu da shi, abin da suka samu shi ne ganyen baure, suka dinka suka kuma rufe tsiraicinsu da su; mun sani irin wannan shiri na mutum ba zai kai shi ko’ina ba; domin idan suka dinka ganyen baure, misali da safe, kafin rana ta fadi zai bushe, dole kuma su nemi wani ganyen su dinka mai yiwuwa kafin yamma ta yi sun canja har sau biyu ko uku ko fiye da haka. Ganye ba zai dade ba.