Zulum, El-Rufai da Buni za su a jagoranci kwamitocin babban taron APC
Gwamnan Neja zai jagoraci tantance masu neman takarar shugaban kasa a babban taron
Jam’iyyar APC mai mulki ta nada Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum da Gwamnan Kano, Abdullahi a jergi shugabannin kwamitocin babban taronta da ke tafe ranar Litinin.
Daga cikin kwamitocin wucin gadi 18 da uwar Jam’iyyar APC ta kafa, Zulum zai jagoranci Kwamitin Sufuri, a yayin da Ganduje ke jagorantar Kwamitin Samar da Masaukin Baki.
Da yake sanar da kafa kafa kwamitoci, Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar APC, Barist Felix Morka, ya ce Kwamitin Sauraran Korafe-korafen Bayan Zabe zai kasance a karkashin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.
Gwamnan Jihar Kebbi wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Atiku Bagudu, shi ne Shugaban Kwamitin Tsare-tsaren Zaben Dan Takarar Shugaban Kasa.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, shi ne ke jagorantar Kwamitin Gudanarwa da Shirye-shiryen Gabanin Zabe da kuma Daukar Bayanai.
Kwamitin Kudade da Zirga-zirga zai kasance a karkashin Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu; sai Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya da aka nada Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi.
Shi kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong shi ne Shugaban Kwamitin Walwala da Jin Dadi; Kwamitin Kula da Ayyuka da Wurin Taro kuma a karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara.
Ministan Kwadago, Dokta Chris Ngige, shi ne Shugaban Kwamitin Kula da Lafiya, sai Kwamitin Shari’a karkashin jagorancin Ministan Shari’a Abubakar Malami (SAN).
Shugaban Kwamitin Yada Labarai shi ne Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; Kwamitin Iso a karkashin Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina; sai Kwamitin Sadarwa na Zamani na hannun Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq.
Sai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, da zai jagoranci Kwamitin Tantance Jakadu a wurin taron.