Zulum ya ƙaddamar da dashen itatuwa miliyan 10 a Borno
Zulum ya kaddamar da aikin ne a garin Kawuri da ke Karamar Hukumar Konduga.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya kaddamar da aikin dashen itatuwa miliyan 10 a Jihar Borno.
Wakilinmu ya ruwaito cewa an kaddamar da wannan gagarumin aikin ne domin yaki da kwararowar hamada da kuma bunkasar muhalli a jihar a wannan shekara ta 2024.
- Cafke sojan da ya harbe matashi a Zariya abun a yaba ne — Atiku
- ‘Yan fansho za su samu haƙƙoƙinsu bayan shekara 21 a Neja
Zulum ya kaddamar da aikin ne a garin Kawuri da ke Karamar Hukumar Konduga, a wani bangare na dabarun maido da muhallin jihar tare da dakile illolin sauyin yanayi.
A cewar gwamnan, matakin wani mataki ne na magance matsalolin muhalli a jihar, wanda kwararowar hamada da tashe-tashen hankula suka haifar.
“Mun himmatu wajen kare muhallinmu da kuma inganta ci gaba mai dorewa,” in ji Gwamna Zulum.
“Wannan aiki na shuka itatuwa yana da mahimmanci don maido da yanayin mu da kuma tabbatar da dorewar makomar muhallin mu.”
Hukumar Kula da Dashen Itatuwa da Yaki da Dumamar Yanayi ta NAGGW ta yaba wa Jihar Borno bisa jagorancin da take yi a fannin kare muhalli.
NAGGW ta kuma tabbatar da kokarin da take yi na kafa reshenta a Jihar Borno wanda take fatan za ta fadada a sauran jihohi.
Masana muhalli sun yaba da shirin a matsayin “mai canza yanayi a yankin da ake da ake fuskantar kwararowar hamada da dumamar yanayi, inda suka bukaci sauran jihohin kasar da su yi koyi da Jihar Borno.