Zulum ya ba da N20m ga iyalan sojan da aka kashe
Sakamakon kisan da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi wa wani kwamandan rundunar sojin Najeriya, Gwamnatin Jihar Borno ga bai wa iyalan mamacin gudunmuwar gida da naira miliyan 20 domin su ci gaba daukar nauyin kansu. A ranar Talata Gwamna Babagana Zulum ya sanar da cewa za a gina wa marayu da matar marigayi Kanar […]
Sakamakon kisan da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi wa wani kwamandan rundunar sojin Najeriya, Gwamnatin Jihar Borno ga bai wa iyalan mamacin gudunmuwar gida da naira miliyan 20 domin su ci gaba daukar nauyin kansu.
A ranar Talata Gwamna Babagana Zulum ya sanar da cewa za a gina wa marayu da matar marigayi Kanar Dahiru Chiroma Bako wadataccen gida da za su ci gaba da rayuwarsu a ciki.
Ya ce, “Muna taya su jimami kuma babu abin da za a yi musu da zai zamo kwatankwacin rayuwarsa.
“Ina sanar da cewa Gwamnatin Jihar Borno za ta gina musu gida wadatacce.
- Boko Haram ta kashe Kanar din sojan Najeriya
- Boko Haram: Manoma miliyan 1 ba sa iya fita gona a Borno
“Na samu labarin cewa Rundunar Sojin Kasa karkashin jagorancin Laftanar Janar Tukur Buratai za ta dauki nauyin karatun ’ya’yansa, saboda haka za mu kara tallafa wa iyalansa a kan na rundunar sojin”, inji gwamnan.
Kanar Chiroma na daga cikin mutane da dama da mayakan Boko Haram suka hallaka a hare-haren da suka kai sassan Jihar Borno a karshen makon jiya.
A daya daga cikin hare-haren ne mayakan suka kashe wasu sojoji tare da raunata Kanar Chiroma, wanda daga baya ya ce ga garinku nan a gadon asibiti.
Gwamna Zulum yayin halartar jana’izar mamacin a ranar Talata, ya misalta shi a bayyana shi a matsayin jarumi kuma gwarzo wannda mutuwarsa rashi ne ga jihar Borno da kuma Najeriya baki daya ba ga iyalansa da rundunar sojin ba.