Zulum ya sa a rushe gidajen karuwai a kwace filayensu

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya ba da umarnin rushe gidajen karuwai da matattarar bata-gari da ke unguwar Bayan Quarter, a garin Maiduguri cikin awa 72, ya kuma kwace filayen

Zulum ya sa a rushe gidajen karuwai a kwace filayensu

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya ba da wa’adin awa 72 a rushe gidajen karuwai da matattarar bata-gari a Maiduguri, babban birnin jihar.

Zulum ya ba wa gidajen karuwan awa 12 su san inda dare ya yi musu, ya kuma kwace filayensu, wadanda a baya gwamnatin jihar ta ba wa hukumar jiragen kasa ta Najeriya.

Ya sanar da haka ne a lokacin da ya kai ziyar gani da ido a unguwar ‘Bayan Quarters’ wadda ta yi -kaurin suna da gidajen mata da ayyukan daba da masu shaye-shaye a garin na Maiduguri.

Gwamnan ya alakanta yawaitar aikata miyagun laifuka da yaduwar gidajen karuwai da matattarar bata-gari da shaye-shayen miyagun kwayoyi da suaransu.

A cewarsa, wadannan miyagun ayyukan na barazana ga zaman lafiya da kuma tarbiyya a cikin al’umma, musamman ganin yadda gidajen matan ke da kananan yara da ke karuwanci.

“Gwamnati ta samu rahoton abin da ke faruwa a nan wurin don haka haramtaccen wuri ne, inda ake kashe mutane, ake kyankyashe ’yan ta’adda, don haka na ba da umarnin kowa ya tashi,” in ji Zulum.

Ya ce kwace filayen ya zama dole, ganin yadda hukumar jiragen kasar ke ba da hayar filayen ga masu aikata laifi da tattara bata-gari.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna