Zulum ya ba iyalan Janar din sojan da aka kashe a Borno N20m
Zulum da sanatocin jiharsa sun jajanta wa iyalan sojojin da suka rasu a harin ISWAP.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya kai ziyarar ta’aziya ga iyalan marigayi Birgediya-Janar Dzarma Zirkusu wanda mayakan kungiyar ISWAP suka kashe a Jihar Borno.
A ranar Laraba ce gwamnan jagoranci daukacin sanatocin jihar masu ci, zuwa gidan mamacin da ke barikin sojoji na Ribadu da ke Kaduna, inda , inda suka jajanta musu, ya kuma ba su tallafin Naira miliyan 20.
- Amurka ta cire Najeriya daga jerin kasashen da ke tauye ’yancin yin addini
- Bayan gargadin Buhari ’yan bindiga sun kashe mutum 15 a Sakkwato
Mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau, ya sanar da cewa gwamnan zai kuma bayar da kwatankwacin tallafin ga iyalan kananan sojoji uku da suka kwanta dama tare da Janar Dzarma a musayar wutar da suka yi da ’yan ta’addan.
Zulum ya kai ziyarar ta’aziyyar a Kaduna ne tare da ’Yan Majalisar Dattawa Jihar Borno masu ci, da kuma ’yan Majalisar Dokokin Jihar Borno biyu, masu wakiltar mazabar Chibok da Askira Uba, inda Janar Dzarma da dakarun nasa suka gamu da ajalinsu.
A lokacin ziyarar, gwamnan ya gana da mai dakin Janar Dzarma da ’ya’yansa biyar da kuma dan uwan mamacin, inda ya jajanta musu gami da yaba wa jarumtar mamatan.
Babban Kwamandan Runduna ta Daya ta Sojin Kasan Najeriya, Birgediya-Janar T. Opuene tare da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, su ne suka tarbi Zulum da tawagar tasa, kafin suka zarce zuwa gidan marigayin.