Zulum ya bai wa jami’an tsaro kyautar gidaje da motoci a Borno
Gwamnan ya ce zai ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro domin su samu damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa jami’an ‘yan sanda kyautar gidaje 280 tare da bayar da gudunmuwar motoci 110 da babura 500 domin inganta tsaro a jihar.
Wannan shiri na da nufin inganta jin daɗin jami’an tsaro da kuma ƙarfafa yaƙi da aikata laifuka da ta’addanci.
A wajen bikin rabon kayayyakin a Maiduguri, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya jinjina wa gwamna Zulum kan goyon bayansa ga jami’an tsaro.
Ya ce wannan tallafi mataki ne mai kyau wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Borno.
“Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen kula da jin daɗin jami’an da ke sadaukar da rayuwarsu don kare al’umma,” in ji Zulum.
“Waɗannan motoci za su taimaka wajen inganta zirga-zirga da hanzarta kai ɗauki a lokacin buƙata.”
Egbetokun ya bayyana wannan gudunmuwa a matsayin wani babban ci gaba.
“Wannan tallafi zai ƙarfafa gwiwa da inganta ayyukan jami’anmu,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma gode wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa jagorancinsa wajen tallafa wa jami’an tsaro.
Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da kayan aiki da duk wani abu da zai taimaka wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Manyan jami’an tsaro, ciki har da shugabannin ’yan sanda da sojoji, sun halarci taron, inda suka jaddada buƙatar haɗin gwiwa don tunkarar ƙalubalen tsaro a jihar.
Ga hotunan a ƙasa: