Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta
Zulum ya ce zai tallafa wa masarautar wajen gyara gine-ginen da Boko Haram suka lalata.
![Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/IMG-20250212-WA0050.jpg)
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya miƙa wa sabon Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi sandar sarauta, a wani biki da aka gudanar a filin wasa na garin Bama.
A yayin bikin, Gwamna Zulum ya yi alƙawarin kammala titin Maiduguri zuwa Banki domin bunƙasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya, Kamaru da Chadi.
- Dokokin gyaran haraji sun tsallake karatu na biyu a majalisa
- An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna
Haka kuma, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kammala Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Bama da kuma dawo da wutar lantarki a yankin.
Zulum, ya ƙara da cewa za a ci gaba da tallafa wa masarautar da gyara gine-ginen da Boko Haram suka lalata.
Hakazalika, ya ce gwamnatinsa za ta taimaka wajen dawo da ’yan gudun hijira zuwa gidajensu.
A nasa jawabin, sabon Shehun Bama, Umar Kyari Umar El-Kanemi, ya gode wa gwamna Zulum bisa wannan matsayi da ya gaji daga mahaifinsa, Alhaji Ibrahim Umar Ibn Umar El-Kanemi, wanda ya shafe kusan shekaru 30 yana mulkin masarautar Bama.
An yi hawan dawaki, raye-rayen gargajiya, wake-wake da harbe-harben bindiga.
Manyan baƙi da suka halarta sun haɗa da Mataimakan Gwamnonin Borno da Yobe, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, da sauran sarakuna da manyan jami’an gwamnati.