Zulum ya bayyana Gubio a matsayin wanda ya fi so ya gaje shi
Ana ganin cewa wannan goyon baya na iya saɓa wa muradin magoya bayan mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima
Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya bayyana tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, Mustapha Gubio, a matsayin wanda ya fi so ya gaje shi a Zaɓen 2027, a ƙarƙashin inuwar jam’iyyarsu ta APC.
Mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya, ya tabbatar da hakan, yana mai cewa Gubio ya kai wa gwamnan ziyara bayan sayen fom ɗin takara a Abuja.
- Cikin ɗalibai 10 a jami’o’in Najeriya 6 suna harkar damfara ta yanar gizo — EFCC
- DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata
Hakan na zuwa ne bayan wasu hotuna da aka fitar, waɗanda suka nuna Gubio yana gabatar da fom ɗinsa na neman takara ga gwamnan tare da wasu jiga-jigan siyasa, ciki har da Sanata Mohammed Tahir Monguno.
Sai dai wannan mataki ya haifar da muhawara a cikin APC a Borno, inda masu sharhi ke ganin cewa hakan na iya ƙara dagula rikicin cikin gida da ke jam’iyyar.
Masu lura da al’amuran siyasa sun nuna cewa wannan goyon baya na iya saɓa wa muradin magoya bayan mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ke da tasiri a siyasar jihar.

Wasu na ganin cewa akwai yiwuwar rikici tsakanin ɓangarorin siyasa daban-daban, wanda zai iya kawo cikas ga haɗin kan jam’iyyar kafin zaɓen fidda gwani.
Shigar Gubio cikin sahun manema takarar ya ƙara faɗaɗa jerin ‘yan takara a APC, lamarin da ka iya haifar da fafatawa mai zafin gaske a zaɓen fidda gwani da za a gudanar.