Zulum ya bukaci a tura jami’an SARS Borno

Zulum ya ce SARS ta yi rawar gani a yaki da Boko Haram a Jihar Borno don haka yana neman a tura jami’anta can

Zulum ya bukaci a tura jami’an SARS Borno

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya bukaci a tura jamia’n rusasshiyar runduar ‘yan sanda ta SARS domin taimaka wa yaki da Kungiyar Boko a Jihar.

Da yake karbar bakuncin Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, gwamnan ya ce jami’an SARS sun yi abin a yaba a yaki da Boko Haram a jihar.

Gwamnan ya yi kiran ne bayan gwamnan ya yi kiran ne bayan wasu gungiyoyi a jihar sun gudanar da zanga-zangar lumana ta goyon bayan SARS wadda aka yi kwanaki ana zanga-zanga a sassan Najeriya domin a rushe ta.

Zulum said, in Borno state, SARS had made remarkable achievements against Boko Haram.

A jawabinsa Aregbesola ya shaida wa gwamnan cewa ya ziyarci jihar ne domin samun bayanin hakikin yanayin tsaro a jihar.

Ya kuma yaba a Gwamna ZUlum bisa tsayin dakan da ya yi domin ganin an samu tsaro da zaman aminci a jihar Borno.

Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo