Zulum ya dakatar da ma’aikatan asibitin Ngala

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya dakatar ma’aikatan da ke aiki a wani asibiti saboda sakaci da aiki. Gwamna Zulum da kansa ya sanar da dakatar da albashin dukkan likitoci da ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan Babban Asibitin garin Ngala, saboda sun yi watsi da daruruwan marasa lafiya wadanda galibinsu ‘yan gudun hijira ne. […]

Zulum ya dakatar da ma’aikatan asibitin Ngala

Gwamna Babagana Zulum

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya dakatar ma’aikatan da ke aiki a wani asibiti saboda sakaci da aiki.

Gwamna Zulum da kansa ya sanar da dakatar da albashin dukkan likitoci da ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan Babban Asibitin garin Ngala, saboda sun yi watsi da daruruwan marasa lafiya wadanda galibinsu ‘yan gudun hijira ne.

“Gwamnan Borno ya dakatar da dukkan ma’akatan asibitin Ngala, saboda barin marasa lafiya a hannun kungiyar agaji,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa ba Twitter.

Dakatar da ma’aikatan ta biyo bayan ziyarar ba-zata da Gwamna Zulum ya kai asibitin a ranar Litinin inda ya iske jami’an lafiyan wata kungiyar agaji ta kasashen duniya ne ke kula da majinyatan.

Har zuwa karfe 11 na safe babu ko daya daga cikin ma’aikatan asibitin da ya zo aiki, lamarin da ya sa gwamnan daktar da su saboda yi wa aikinsu rikon sakainar kashi duk da cewar ana biyansu hakkokinsu yadda ya kamata.