Zulum ya janye dokar hana fita a Borno

Bayan tuntubar jami’an tsaro mun dage dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yau Asabar.

Zulum ya janye dokar hana fita a Borno

Gwamnatin Jihar Borno ta dage dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta sanya wa mazauna birnin Maiduguri da kewaye.

Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamnatin Borno ta sanya dokar hana fitar ce biyo bayan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar soma ranar Alhamis a fadin kasar, inda ta rikide zuwa tarzoma.

Sai dai a cikin wata sanarwa da Gwamna Babagana Zulum ya fitar kai tsaye, ya bayyana cewa, “saboda kwanciyar hankali, gwamnati tare da tuntubar jami’an tsaro ta dage dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yau Asabar 3 ga Agusta, 2024.

“Mun yi hakan ne don bai wa mazauna yankin damar fitowa da misalin karfe 6 na safe domin fara harkokinsu na yau da kullum cikin tsari.

“Abin takaici ne yadda wasu bata-gari suka yi amfani da zanga-zangar wajen sace kayan mutane tare da barnata dukiyoyin gwamnati da na jama’a wanda wannan lamari ne da gwamnatin ba za ta taba amince da shi ba.

“Duk da cewa an dage dokar hana fita a yanzu, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar mataki kan duk wanda ya karya doka da oda da sunan zanga-zanga,” a cewar Zulum.

Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja