Zulum ya kaddamar da taron gyara karatun tsangaya a Borno
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da taron gyara tsarin harkokin ilimin Almajiranci da aka fi sani da tsangaya a Arewacin Najeriya. Taron wanda aka gudanar a dakin taro na Sakatariyar Musa Usman da ke Maiduguri na neman kawar da tsattsauran da mummunar fahimtar ilimin addinin musulunci da ya taimaka wajen bullowar mayakan Boko […]
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da taron gyara tsarin harkokin ilimin Almajiranci da aka fi sani da tsangaya a Arewacin Najeriya.
Taron wanda aka gudanar a dakin taro na Sakatariyar Musa Usman da ke Maiduguri na neman kawar da tsattsauran da mummunar fahimtar ilimin addinin musulunci da ya taimaka wajen bullowar mayakan Boko Haram.
- ’Yan bindiga sun sace mutane, sun kashe wasu 2 a Sakkwato
- Lakurawa sun tsere bayan sojoji sun ragargaje su a Kebbi
Zulum ya bayyana cewa manufar taron shi ne magance matsalolin rashin tsaro ta hanyar ilimi ga daukacin al’ummar Jihar Borno.
“Don ganin an cimma hakan, gwamnatin Jihar Borno ta kafa hukumar kula da ilimin larabci da tsangaya, inda ta bullo da tsarin karatun bai daya na makarantun tsangaya da na Islamiyya.
A cewarsa, “wannan tsari ya hada da manyan kwalejojin Islama da ke kula da yaran da ke almajiranci da ya hada manhajoji na addini da na boko wuri guda.
“Sake fasalin tsangaya zai bai wa almajiri kyakkyawar dama a rayuwa kasancewar manufar gwamnati ita ce daidaita tsarin ilimi na yau da kullun zuwa ingantattun makarantun tsangaya don shiga kwaleji da jami’a,” in ji Zulum.
A jawabinsa, Shugaban Hukumar Ilimin Larabci da Tsangaya ta Jihar Borno, Sheikh Arabi Abulfatahi, ya gode wa Gwamna Zulum bisa tallafin da ya bayar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa sauran manyan baki da suka gabatar da jawabin yi wa tsarin almajiranci garambawul a yayin taron sun hada da Farfesa Mustapha Gwadabe da Mohammed Alhaji.
Taron ya tattaro masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, da malaman addini, da masu fafutukar kare hakkin al’umma, domin tattaunawa kan hade almajiranci da ilimin boko.