Zulum ya lashe zabe a kananan hukumomi 7 na Borno
Kananan hukumomin sun hada da Kaga, Magumeri, Mafa, Dikwa, Jere, Ganzai and Guzamala.
Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Borno.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fara tattara sakamakon zaben gwamna a Borno, inda Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ke kan gaba da kuri’a 132,526.
Zulum ya samu kuri’un ne a kananan hukumomi 7 daga cikin 27 da jihar ke da su kamar yadda baturen zaben jihar.
- INEC za ta gudanar da karashen zaben Delta ranar Lahadi
- Dan shekara 35 ya kayar da Shugaban Majalisar Dokokin Yobe
Kananan hukumomin sun hada da Kaga, Magumeri, Mafa, Dikwa, Jere, Ganzai and Guzamala.
Farfesa Jude Rabo ya bayyana a cibiyar tattara sakamakon da ke Kwalejin Ilimi ta Kashim Ibrahim da ke Maiduguri, babban birnin jihar.