Zulum ya raba tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Borno

Tallafin na zuwa ne biyo bayan ambaliyar ruwa da ta shafe wasu sassan Maiduguri.

Zulum ya raba tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Borno

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya fara rabon kayan tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.

Waɗanda abin ya shafa suna zaune a sansani kusan 36 bayan da ambaliyar ta taso daga dam ɗin ruwa na Alau, wanda ya tilastawa kusan mutum miliyan biyu barin gidajensu a Maiduguri da kewaye.

An gudanar da rabon tallafin a ranar Litinin, a sansanin Bakasi da ke kan titin Damboa a Maiduguri.

Kayan tallafin da aka bai wa waɗanda abin ya shafa sun haɗa da buhun shinkafa na nauyin kilogiram 25, katon ɗin taliya, da kuma kuɗi Naira 10,000.

Da yake magana da manema labarai, Gwamna Zulum, ya nuna damuwa kan yadda wasu mutane da ambaliyar ba ta shafa ba suke tururuwa zuwa sansanin don karɓar tallafi.

“Mun lura cewa ba zai yiwu mu ci gaba da karɓar mutane a sansanoni ba saboda da yawan wasu ambaliyar ba ta shafe su ba,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma sanar da shirye-shiryen gudanar da cikakken bincike a yankunan da abin ya shafa don tsara yadda za a ba su ƙarin tallafi ya yi nisa.

“Mun yanke shawarar tara dukkanin kayan da ake buƙata don tabbatar da cewa duk wanda ambaliyar ta shafa ya samu tallafin.

“Mun kuma kammala shirin yin bincike don tabbatar da adadin waɗanda abin ya shafa,” a cewarsa.

Darakta Janar ta Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Zubaida Umar, ta kuma yi tsokaci kan irin tallafin da hukumarta ta bai wa waɗanda ambaliyar ta shafa.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja