Zulum ya rufe sansanin ’yan gudun hijira mafi girma a Bama

Zulum ya nuna damuwa kan ƙaruwar ayyukan laifi a wasu sansanonin ’yan gudun hijira, yana mai gargaɗin cewa mayaƙan Boko Haram da na ISWAP na ci gaba da kutsawa cikin sansanonin

Zulum ya rufe sansanin ’yan gudun hijira mafi girma a Bama

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin rufe sansanin ’yan gudun hijira da ke Bama nan take, wanda shi ne mafi girma a wajen Maiduguri, babban birnin jihar.

Zulum ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a Gwoza bayan ya kai ziyara Sansanin ’Yan Gudun Hijira da ke Makarantar Sakandaren Gwamnati.

Ya kuma bayyana cewa za a rufe sansanin ’yan hijira na Gwoza cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa.

“Mun ziyarci Bama jiya, inda muka sa ido kan tantance ’yan gudun hijira. Zuwa tsakar rana yau, ya kamata a rufe sansanin Bama. Mun kuma tantance ’yan gudun hijira na Gwoza, kuma in Allah Ya yarda, za a rufe wannan sansani cikin makonni biyu ko uku masu zuwa,” in ji shi.

Gwamnan ya ce an samu damar ɗaukar wannan mataki ne sakamakon dawowar zaman lafiya a yawancin yankunan da a baya mayaƙan Boko Haram suka mamaye.

A cikin shekaru bakwai da suka gabata, Gwamnatin Jihar Borno ta mayar da ’yan gudun hijira zuwa garuruwansu a yankuna da dama na Ƙaramar Hukumar Bama, ciki har da Darajamal, Nguro Soye, Goniri, Banki, Abbaram, Ngoshe, Kirawa da Warabe.

 

’Yan Boko Haram sun sake a cikin ’yan gudun hijira — Zulum

Sai dai Zulum ya nuna damuwa kan ƙaruwar ayyukan laifi a wasu sansanonin ’yan gudun hijira, yana mai gargaɗin cewa mayaƙan Boko Haram da na ISWAP na ci gaba da kutsawa cikin sansanonin.

“Akwai ayyukan laifi da ke gudana a sansanonin. Mun gano waɗanda ke da hannu a ciki, kuma za mu mayar da su zuwa garuruwansu ƙarƙashin kulawar shugabannin al’ummominsu,” in ji gwamnan.

Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda wasu mutane ke barin garuruwansu su koma sansanoni domin samun kayan tallafin da ƙungiyoyin agaji masu zaman kansu ke rabawa.

A cewarsa, aikin tantancewar ya gano cewa akwai mutane da dama da ke iƙirarin kasancewa ’yan gudun hijira alhali ba haka ba ne, lamarin da ya sa gwamnati ba za ta iya ci gaba da kula da sansanonin ba.

Ya ƙara da cewa kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa za a rufe wasu sansanonin ’yan gudun hijira a sassan jihar, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shirin mayar da mutane garuruwansu cikin tsari mai ɗorewa.