Zulum ya sanya hannu kan kasafin 2025 na N615.8bn
Gwamnan ya gode wa Majalisar Dokokin jihar kan amincewa da kasafin kuɗin cikin gaggawa.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sanya hannu kan kasafin shekarar 2025 na Naira biliyan 615.8, wanda aka ƙara Naira biliyan 31.1 a kai.
Gwamnan ya sanya hannu kan kasafin ne a ranar Litinin bayan Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abdulkarim Lawan, ya miƙa masa ƙudirin a Maiduguri.
- Miji da mata sun zama Farfesa a tare a BUK
- Sojoji sun hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga, Sani Rusu a Zamfara
Zulum, ya yaba wa Majalisar Dokokin Jihar kan amincewa da kasafin cikin gaggawa, tare da yin kira ga shugabannin ma’aikatu da hukumomi su bi tanade-tanaden kasafin yadda ya kamata.
“Mun gode wa shugabanci da haɗin kan Majalisa. Ba za mu cimma nasarorin da muka samu ba, ba tare da goyon bayansu ba,” in ji Zulum.
Kakakin Majalisar, Lawan, ya yaba wa gwamnan kan nasarorin gwamnatinsa cikin shekaru shida da suka gabata.
Ya bayyana cewa ƙarin kasafin ya zama dole domin magance matsalolin da suka shafi al’umma.
“Ƙarin da aka yi ya zama dole domin inganta rayuwar jama’a,” in ji Lawan.
Bayan sanya hannu kan kasafin, Zulum ya jagoranci taron farko na Majalisar Zartarwa na bana.
A yayin taron ya gode wa tawagarsa bisa jajircewa tare da bayyana Dokta Mustapha Mallumbe a matsayin Mataimakin Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnati.
Mallumbe ya maye gurbin Farfesa Hussaini Marte, wanda ke fama da rashin lafiya.