Zuma ta tarwatsa ’yan kwallo a Tanzaniya
Kudajen zuma sun tarwatsa ’yan kwallo da alkalan wasa da kuma magoya baya a filin wasa da na Uhuru Stadium da ke Dares- Salam a kasar Tanzaniya a ranar Asabar da ta gabata. Rahoton da jaridar Mwananchi da ake wallafawa a kasar ta kalato, ya ce a daidai minti 10 da dawowa daga hutun rabin […]
Kudajen zuma sun tarwatsa ’yan kwallo da alkalan wasa da kuma magoya baya a filin wasa da na Uhuru Stadium da ke Dares- Salam a kasar Tanzaniya a ranar Asabar da ta gabata.
Rahoton da jaridar Mwananchi da ake wallafawa a kasar ta kalato, ya ce a daidai minti 10 da dawowa daga hutun rabin lokaci ne kudajen zumar suka mamaye filin a lokacin da ake wasa a tsakanin kulob din Young Africans da ake wa lakabi da Yanga da kuma na Iringa United. Nan take ’yan kwallo da alkalan wasa da kuma ’yan kallo suka nemi mafaka inda wasa ya tsaya cik.
Rahoton ya ce dan kwallon kulob din Yanga, Ali Mtoni Sonso ne kadai ya samu rauni yayin da sauran suka tsira.
Bayan an shafe kimanin minti 10 ne da bayyanar kudajen zumar aka ci gaba da wasan, amma da yawa daga cikin magoya baya ba su koma filin don ganin yadda wasan zai kaya ba.