Zumunci da fa’idarsa ga rayuwar al’umma (1)

Tare da sallama, kamar yadda aka saba nake bude wannan fili a wannan mako. Jama’a, Assalamu alaikum. Kamar yadda filin yake, yau kuma za mu yi kokarin yi mana tambihi ne da jawo hankulanmu domin mu gane tasirin da ke cikin zumunta. Kuma za mu duba irin kima da muhimmancin da ke tattare da daraja […]

Zumunci da fa’idarsa ga rayuwar al’umma (1)
Zumunci da fa’idarsa ga rayuwar al’umma (1)

Tare da sallama, kamar yadda aka saba nake bude wannan fili a wannan mako. Jama’a, Assalamu alaikum. Kamar yadda filin yake, yau kuma za mu yi kokarin yi mana tambihi ne da jawo hankulanmu domin mu gane tasirin da ke cikin zumunta. Kuma za mu duba irin kima da muhimmancin da ke tattare da daraja zumunci. Domin kuwa duk wanda ya ce zai rayu ba tare da zumunci ba, to zai kasance kamar wani matafiyi a cikin sahara, shi kadai, babu gida gaba kuma babu gida baya, balle kuma ya samu mutumin da zai yi ko da hira da shi.

Ita dai zumunta ta samo asali ne tun farkon halitta, musamman idan muka lura da yadda rayuwar shi kansa mutum ta faro. Kowa dai ya dade da sanin cewa daga tsatson mutane biyu duk al’umma ta samu, wato Adamu da Hauwa’u. Idan ma muka kara yin wani lissafin, sai mu gane cewa daga mutum daya duk muka samu, domin ita kanta Hauwa’un, daga shi kakan namu Adamu ta samu. Kuma tun daga wannan lokaci ne zumunci ya tabbata.
Kowane dan Adam dan uwan wani ne, dan wani ne, kanen wani ne, yayan wani ne ko kuma baban wani. Idan kuma zumuntar ta canza fasali, yana iya kasancewa abokin wani, na nesa ko na kusa. Babu ko shakka kowa na bukatar kowa ta bangaren rayuwa iri daban-daban. Domin kuwa babu wanda zai iya tsinana wa kansa komai shi kadai, dole sai ya samu tallafin wani nasa, na nesa ko kuma na kusa. Wannan ne ya sanya zumunta ta zama dole ga dan Adam, kuma shi ya sanya daraja zumunci ya zama wani bangare na Sinadarin Rayuwa.
Madamar mutum na son ya kasance mai kima, mai mutunci a cikin al’umma, mai cin ribar rayuwa, to ya zama dole ya rika daraja zumunci. A nan sai mu tambayi kanmu, shin mene ne zumuncin, kuma yaya ake daraja shi? Shi dai zumunci wata irin halayya ce ta kwarai, wacce ke sadar da dangantaka ta nasaba tsakanin ’yan uwa ko bare. Zumunci ne ke kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da fahimtar juna tsakanin al’umma.
Ta hanyar da mutum zai bi ya inganta zumunci shi ne, sai ya gano yadda yake, sannan ya gano dangantakarsa da mutanen da yake rayuwa a cikinsu, na jini da bare, na kusa da na nesa. Ta haka ne mutum zai gane irin yadda zumuntarsa da mutum za ta kasance, domin kowa na da irin nasa hakkin zumuntar daban da ta wani. Alal misali, yadda mutum zai kasance tsakaninsa da mahaifansa, ba haka zai kasance da kannensa ko yayyensa ba. Yadda zai gudanar da zumunci tsakaninsa da matarsa, ba haka zai yi da makwafcinsa ba. Haka kuma yadda zai yi da abokinsa ba haka zai yi da wani na nesa ba, kowa dai na da iya kimar zumuncin da zai gudanar a tsakaninsa da wani.
Kamar yadda Hausawa suka ce, zumunta a kafa take, to wannan gaskiya ne, domin kuwa daya daga cikin manyan ginshikan zumunta shi ne ziyartar juna. Idan ka kula da zumunci ne za ka niki gari zuwa gidan abokinka ko dan uwanka, musamman domin ganin yadda yake. Wannan ziyara kawai, ita ke haddasa kauna da mutunci mai dorewa a tsakanin al’umma.
Zumunta kuma ba ta da sharadin cewa wane na da kaza ko bai da kaza. Ya dace duk matsayin da mutum yake, na farin ciki koma na bakin ciki, na talauci ko na wadata, a yi zumunci da shi. Domin kuwa wanda ke da wadata, sai ya tada marar ita, mai karancin ilimi sai ya koya daga mai ilimi. Mai kaifin basira da fahimtar rayuwa, sai ya shawarci abokin zumuntarsa hanyar da zai bi ya tsira a rayuwarsa.
A nan, ya zama dole mu tsarkake zukatanmu, mu rika yada zumunci ko da ta hanyar wasika ne, balle kuma ga nesa ta zo kusa, ko da ta wayar salula mutum na iya sada zumunta da dan uwansa da ke kuryar duniya. Haka kuma, idan ana zaune wuri daya, alama ce ta karfafa zumunta, mutum ya san halin da dan uwansa ko makwafcinsa yake ciki. Kada mutum ya kasance don yana matsayin attajiri, amma ka ga bai san sunan makwafcinsa ba, don kawai shi makwafcin kila bai da kumbar susa.
Ba daidai ba ne yadda wasu daga cikin mutane ke yi wa zumunta rikon sakainar kashi. Za ka ga ba a son kai ziyara wajen dan uwa na jini, kawai don kila bai da kudi, ko kuma ka ga ana kyamar dan uwa idan ya kawo ziyara ga mutum wanda yake mai hali, don zaton cewa kila don kudinsa ya zo. Duk wannan ba daidai ba ne, kuma ba hanya ba ce ta kwarai da ta dace da muradin zumunci.
Kamar yadda na ce ne daga farko, dukkan mutane ’yan uwan juna ne, kuma kowa na bukatar kowa. Ya zama wajibi mu tsare zumunta, ba tare da wani la’akarin bambancin yanayin rayuwa ba. Duk wanda ya daraja zumunta, to kuwa ya rufa wa kansa asiri, kuma ya dauki wata babbar turba, wacce za ta kai shi ga tudun mun tsira. Kuma duk wanda ya kasance mai zumunci na ka’ida ba na ganin wani abu ba, to lallai shi ne ya zizara wa rayuwarsa babban sinadarin daukaka rayuwarsa cikin mutunci da kaunar al’umma.
Zumunci kuma wata irin itaciya ce mai albarka, wacce ke baza rassanta, mai yalwata inuwarta ga al’umma, wacce ke kashe duk wani yanayi na rashin dacewa. Ita kanta zumunta ta zahiri, ba ta dagogwarago ba, tana magance masifu da bala’o’in rayuwa. Ke nan dai zumunta ce sirrin ci gaban al’umma. Ita ce kuma tushen yalwar arziki da tabbatar da zaman lafiya a cikin kasa. Don haka, ya ’yan uwa, mu rika daraja zumunta a kowane lokaci!