Zumunci da fa’idarsa ga rayuwar al’umma (2)

A makon jiya ne muka faro wannan maudu’i, yau kuma za mu karkare shi da ikon Allah.  Kamar yadda Hausawa suka ce, zumunta a kafa take, to wannan gaskiya ne, domin kuwa daya daga cikin manyan ginshikan zumunta shi ne ziyartar juna. Idan ka kula da zumunci ne za ka niki gari zuwa gidan abokinka […]

Zumunci da fa’idarsa ga rayuwar al’umma (2)

A makon jiya ne muka faro wannan maudu’i, yau kuma za mu karkare shi da ikon Allah. 

Kamar yadda Hausawa suka ce, zumunta a kafa take, to wannan gaskiya ne, domin kuwa daya daga cikin manyan ginshikan zumunta shi ne ziyartar juna. Idan ka kula da zumunci ne za ka niki gari zuwa gidan abokinka ko dan uwanka, musamman domin ganin yadda yake. Wannan ziyara kawai, ita ke haddasa kauna da mutunci mai dorewa a tsakanin al’umma.

Zumunta kuma ba ta da sharadin cewa wane na da kaza ko bai da kaza. Ya dace duk matsayin da mutum yake, na farin ciki ko ma na bakin ciki, na talauci ko na wadata, a yi zumunci da shi. Domin kuwa wanda ke da wadata, sai ya ta da marar ita, mai karancin ilimi sai ya koya daga mai ilimi. Mai kaifin basira da fahimtar rayuwa, sai ya shawarci abokin zumuntarsa hanyar da zai bi ya tsira a rayuwarsa.

A nan, ya zama dole mu tsarkake zukatanmu, mu rika yada zumunci ko da ta hanyar wasika ce, balle kuma ga nesa ta zo kusa, ko da ta wayar salula mutum na iya sada zumunta da dan uwansa da ke kuryar duniya. Haka kuma, idan ana zaune wuri daya, alama ce ta karfafa zumunta, mutum ya san halin da dan uwansa ko makwabcinsa yake ciki. Kada mutum ya kasance don yana matsayin attajiri, amma ka ga bai san sunan makwabcinsa ba, don kawai shi makwabcin kila bai da kumbar susa.

Ba daidai ba ne yadda wadansu daga cikin mutane ke yi wa zumunta rikon sakainar kashi. Za ka ga ba a son kai ziyara wajen dan uwa na jini, kawai don kila bai da kudi, ko kuma ka ga ana kyamar dan uwa idan ya kawo ziyara ga mutum wanda yake mai hali, don zaton cewa kila don kudinsa ya zo. Duk wannan ba daidai ba ne, kuma ba hanya ba ce ta kwarai da ta dace da muradin zumunci.

Kamar yadda na ce ne daga farko, dukan mutane ’yan uwan juna ne, kuma kowa na bukatar kowa. Ya zama wajibi mu tsare zumunta, ba tare da la’akari da wani bambancin yanayin rayuwa ba. Duk wanda ya daraja zumunta, to kuwa ya rufa wa kansa asiri, kuma ya dauki wata babbar turba, wacce za ta kai shi ga tudun mun tsira. Kuma duk wanda ya kasance mai zumunci na ka’ida ba na ganin wani abu ba, to lallai shi ne ya zizara wa rayuwarsa babban sinadarin daukaka rayuwarsa cikin mutunci da kaunar al’umma.

Zumunci kuma wata irin itaciya ce mai albarka, wacce ke baza rassanta, mai yalwata inuwarta ga al’umma, wacce ke kashe duk wani yanayi na rashin dacewa. Ita kanta zumunta ta zahiri, ba ta dagogwarago ba, tana magance masifu da bala’o’in rayuwa. Ke nan dai zumunta ce sirrin ci gaban al’umma. Ita ce kuma tushen yalwar arziki da tabbatar da zaman lafiya a cikin kasa. Don haka, ya ’yan uwa, mu rika daraja zumunta  a kowane lokaci!

Mun kammala.