Zunden Zaman-furfuren Zaman-fara
Zaurancen zunden Zaman-furfure Zagaye-zagayen zare-zare Zubin zungure Zungurun zangarniyar zurare Zaman farar ziryar zaftare Zabarin zankade-zankade Zankadaziyya ta shide Zillaziyar zille-zille Zillaziyya ta zille Zogin zungura yai zakwade Ka da a ce nai kade-kade Siyasa ce tai mana gande-gande Wasu za sui lashe-lashe da tande-tande Mikaku sun baude Garkar gayauna an farde […]
Zaurancen zunden Zaman-furfure
Zagaye-zagayen zare-zare
Zubin zungure
Zungurun zangarniyar zurare
Zaman farar ziryar zaftare
Zabarin zankade-zankade
Zankadaziyya ta shide
Zillaziyar zille-zille
Zillaziyya ta zille
Zogin zungura yai zakwade
Ka da a ce nai kade-kade
Siyasa ce tai mana gande-gande
Wasu za sui lashe-lashe da tande-tande
Mikaku sun baude
Garkar gayauna an farde
Ba gara bin zago
Maidan boto ta dago
Harigido hukunci ya tattago
Zaman fargaba aka figo
Zaman furfure aka kago
Yarfen yaren Yarin yanka
Mai tsintsiya ta tsinka
Zaren dauri an yaga
Kuri’u sun yi yaga-yaga
An yi kiki-kaka
Ciniki ne na furfure
Ba-ni-in-ba ka ba kwanare
Kumbiya-kumbiya ta tattare
Sharar mai kwakwa da ’yar laushi a bare
Shigifar shammatar shari’a tai mangare
Hukuncin ga akwai bare-bare
Tufka ce ta warware
Zanzaron zabure-zabure
A daina kobare-kobare
A zo ai gyare-gyare
Matsalar kan akaifa
Sakaci ya sa ta fadada
Ganga-ganga tai kugin kida
Har da rade-radin rada
An zo ana ta kwafa
A zabi-sonka
An zababbaka
An zabge kuri’un zabuka
An kuma samu baraka
An dai yi noman barka
Lamushe gudan bisan kofar hanci
Na adadin kuri’un mutunci
Jaddawalin alkaluman sasanci
Keta haddi ne butulci
Damar jama’a ce tabbaci
Kar a yarda da wawanci
Tanadi ko kukutar kunci
An yi wa-ka-ci-ka-tashi
Soke hakkin al’umma da mashi
Kun ji almubazzarancin shasanci
Masassara
Marasa galihu na mamular masara
Mutane an sha shakara
Mahukunta masu tattara
Mui yunkurin hana fandarar kangara
Baban-burin-huriyya
Hukuncin ga a bibiya
Ko a zauna ba hatsaniya
Al’umma ta san ba danniya
Sai mu kara kwazon juriya
Ka da dai a kagara
Sanwa yanzu aka dora
Ka da mugun aiki ya shahara
Lallai mu zabura
Ai zubeben kwarya ba jira
Yawan yamadidin yarfen yaren Yari da Zaurancen zunden Zaman-furfuren Zaman-fara ya sanya ala tilas farfajiyar makarantar Dodorido da ke cikin Amintaciyar jaridar kasar Haurobiya ta bibiyi kadin Shari’ar shigifar shammatar sha’anin shugabanci a Jihar Zaman-fara, inda aka karbe ragama daga jam’iyyar tsintsiya aka danka wa mai danboto da sanda jirge. Bisa wannan dalilin ne Direban-alli ya jefa alamar tambaya, kan cewa ko dai Jihar Zaman-fara, wadda a ’yan kwanakin da suka arce ta rikide zuwa Zaman-fargaba, har ta sake rikida zuwa Zaman-furfure?
Gwamna gwarangwam Shehin Shehinnai, mutum ne mai FAGAMNIYAR FANGIMA. Domin sanin kowa ne a fadin Haurobiya kan irin yadda ya yi ta gararambar kai-kawo a cikin gida da kasashen ketare, musamman daidai lokacin da Zaman fara ya gagara, har aka koma zaman fargaba; shi kuwa daga Haurubja sai dai ku ji an ce ya cilla, kamar wata mashillara, ya ketare. Sannan ya zo ya yi kwakyariyar kumbiya-kumbiyar kakaba ’yan takara, har suka rikide, suka zame wa jam’iyyar tsintsiya ’YAN TAKA (KARAN DANI), don haka bayan jama’a sun yi jimirin jefa musu kuri’u, sai Shigifar Shari’a ta ce an kauce wa ka’ida, kuma mulkin mulaka’u na ’YAN KAKABE ba shi da wata fa’ida ga al’umma. Hakika na yarda da wannan batu na kotun koli, amma inda takaddamar take, ai jama’ar da suka yi jimirin dangwale ba a yi musu adalci ba.
Haurobiyawa, tabbas babu tantama an damalmala al’amura a DAMA-DAMAR-DAWURWURIN KURDA-KURDA SIYASAR WASAN SAMSON SIYA-SIYA. Wai da farin faraway ma, mene dalilin gudanar da zabi-sonka a jihar da ake zaman fargaba; masu tada kan adda sun tunkari jama’a gaba-da-gaba? Uwa-uba ga LAMUNIN LUSHEWAR LUMANA, har ta kai ga an yi zaman rashin AMINCIN AMANA.
’Yan makaranta masu koyon watsattsaken falle shafukan kundayen Shigifar shari’ar dokokin lauye-lauye, wajibi ne a kan ku, ku tabbatar da aiwatar da muhiman gyare-gyare, amma ba ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege ba. Sanin kowa ne ana yi irin wadannan dokoki ne don doke tsilli-tsillin tsilla-tsilla tsaka-mai-wuya da al’umma ta samu kanta, bisa tsarin zaman-tattakewa ko sasarin sa-in-sar siyasa da turka-turka tauye tattali. Idan kuwa haka lamarin yake, to da wace manufa aka yi wannan danyen hukuncin kakaba MUTANEN-WALLE-WALLE a matsayin masu jagorancin jan ragamar wakilcin al’umma a Jihar Zaman-fara; ko dai cinikin furfure aka yi tsakanin mai danboto da sanda jirge da mai tsintsiya? Idan kuwa haka lamarin yake, ai sai mu ce cefane ya yi kyau, wato dai ba-ni-in-ba-ka babu kwanare, ko?
Muna fatan dai sabon gwamna gwarangwam Mutanen-walle-walle ba zaI bar al’ummar su yi ta kalle-kalle ba, ta yadda za a sake lalen malalen mulkin al’umma a ba su cikakkiyar kariyar rayuka da dukiyoyi. Hasali ma, lallai ne a samu tabbacin kawar da ZULLUMIN ZALUNCIN ZALAMAR ZABARIN ZULLON ZINARIN ZAMAN-FARA!
Duk da cewa Shigifar shari’ar ta shammaci al’umma wajen yin Zaurancen zunden Zaman-furfuren Zaman-fara, wannan ba zai hana a yi gyare-gyare ba, ta yadda za a kauce wa kwata irin wannan kwakyariyar nan gaba, don gudun ka da a haifar da gaba da giba a tsakanin al’umma, musamman daidai wannan lokaci da Baba zai karkare wa’adin mulkinsa zango na karamin lauje. Sannan duk wanda ya ji cewa, ‘wannan hukunci ya nunke al’umma a baibai,’ to sai a tursasa mahukunta su aiwatar da gyaran dokoki, ta yadda ba za a sake yi mana wala-walar walle-walle ba. Don haka sai mu karkare da jefa kalubale ga jagororin al’ummar Jihar Zaman-fara, musamman Yaron-Mama, mai sarautar Sarar-daukar-dawainiyar Bakin-kura da Malam Na ’Yar mai shinkafi. Fakat!