Zurarewar Naira tiriliyan 11 a harkar wutar lantarki
A rahoton kungiyar da ba ta gwamnati ba, mai rajin kare hakkokin zaman takewa da tattalin arziki da tantance gaskiyar ayyuka ta SERAP, cewa Naira tiriliyan 11 da aka fitar da zimmar gyara harkar wutar lantarki a kasar nan ta yiwu gwamnatocin da suka gabata sun kashe su a banza tun daga shekarar 1999. Rahoton […]
A rahoton kungiyar da ba ta gwamnati ba, mai rajin kare hakkokin zaman takewa da tattalin arziki da tantance gaskiyar ayyuka ta SERAP, cewa Naira tiriliyan 11 da aka fitar da zimmar gyara harkar wutar lantarki a kasar nan ta yiwu gwamnatocin da suka gabata sun kashe su a banza tun daga shekarar 1999. Rahoton mai taken: “Daga duhu zuwa duhu: Yadda ’Yan Najeriya ke koduwa da hanci a harkar wutar lantarki,” inda acewarsa, akwai yiwuwar a sake sarayar da wata Naira biliyan 20 a banza nan da shekaru 10 masu zuwa, bisa la’akari da irin almubazzarancin da gwmanati ke yi ta wajen zuba kudi a akai-akai ba tare da nazari ba.
A cewar rahoton, yawan kudin ya hada da kudin gwamnati da kason kamfanoni masu zaman kansu da jarin kyautata zamantakewar al’umma (da hannayen jarin da aka sayar). Rahoton SERAP an gabatar da shi a gaban jama’a Legas. Bisa la’akari da damuwar kan cutar da al’umma kan tabarbarewa harkar wutar lantarki da ta ki ci, ta ki cinyewa a kasar nan da irin makudan kudin da ke zurarewa a harkar, rahoton SERAP na da muhimmanci ganin yadda ya fito da wannan matsala ya bayyanata karara. Rahoton ya tabbatar da zargin da ’yan Najeriya suke yi ta kowace fuska, inda suke ganin harkar samar da wutar lantarki a kasar nan mazurari ne da ke kwashe kudi ba tare da samar da wata fa’ida ba, ta yadda ko nawa aka zuba haka lamarin zai kasance.
Tun farko kowace gwamnati ta soja ce ko farar hula takan nuna fifikon ayyukanta a harkar samar da wutar lantarki. Duk da haka da zarar gwamnatin ta kammala wa’adin mulkinta, ko dai harkar ta tsaya inda take ko kuma ta kara yin kasa warwas. Sai dai a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2015, wato lokutan mulkin Olusegun Obasanjo da Umaru ’Yar’aduwa da Goodluck Jonathan, wanda suka yi daidai da lokacin da aka zuba dimbin dukiyar al’umma a harkar makamashi, kuma ba a samu wani alfanu ba. Wannan shi ne abin da aka fi bijiro da shi a cikin rahoton da ya bayar da tababbatattun hujjoji kan yadda aka salwantar da dimbin kudi a wannan harkar, bisa la’akari da gwamnatoci daban-daban da suka shude.
Misali, kamar yadda yake kunshe a shafi na 65 tabarbarewar al’amuran sun samo tushe ne daga shugabancin Hukumar kula da Harkokin Lantarki ta Najeriya (NERC) karkashin Dokta Ransome Owan, wadda ta fara kawo sauye-sauye a harkar cikin shekarar 2003. Abin da kawai ta cimmawa bai wuce jinka wa ’yan hukumar miliyoyin kudin sallama, wadanda ba a yi aikin samar da su ba. Rahoton ya yi nuni da cewa Gwamnatin Obasanjo ta kashe Dala biliyan 10 kan shirin ingantar wutar lantarki na kasa (NIPP) da wasu Dala biliyan 13da aka zuba a harkar cikin shekara takwas. Duk da haka babu wani kyakkyawan sakamako, tun da wutar lantarki ba ta samu a kasar ba.
Kuma rahoton ya yi karin haske kan nakasun shirin Liyel Imoke na gyara ya lakume Naira biliyan 16, ba tare da samar da wani abin a zo a gani ba.. Abin da ya gabata bai hado da Dala biliyan bakwai da dubu 700 da ya karba a kashin kansa don aiwatar da ayyukan raba wutar lantarkin kan layin Jois zuwa Yola, wanda ba a yi ba. Sannan a rahoto an ambaci abin takaicin da Farfesa Chinedu Nebo ya aikata a matsayins ana Ministan Makamashi, inda ya dauki kaddarar wannan muhimmin sashe a karkashin Kamfanin PHCN ya mikata ga kamfanioni masu zamankansu da suka zuba jari a 1 ga Nuwambar 2013, kuma a wani yanayi na kumbiya-kumbiyar keta doka. Ba abin mamaki ba ne jin cewa rahoton ya bijiro da bukatar ganin an binciki zamanin Farfesa Nebo ta yadda za a kwato makudan kudin da aka karkata akalarsu, a gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a badakalar.
Don haka babu wnai rudanio kan cewa sauye-sauyen da aka bullo da su na bunkasa harkar samar da lantarki a kasar nan na tattare da jimurdar da ke yi masa zagonsa. Shi ya sa babu tsarin da ya kai ga gaci. Wannan shi ne dalilin da ya sanya akwai bukatar gwamnati mai ci yanzu ta jajirce wajen tantance matsalolin da ke tattare da tsarin, musamman ganin yadda rahoton SERAP ya yi tonon silili. Babu ko wata tantama akwai gungunb miyagun da suka yi wa harkar dabaibayi, wanda ke yi wa daukacin gyare-gyaren da aka kawo zagon kasa. Tashin farko ga gwamnati shi ne ta ja kunne duk wanda ke da shirin kawo cikas a wannan harkar, tare da kama duk wanda ke da hannu wajen kassarata. Babu abin da ’yan Najeriya ke bukata fiye da wannan.