Zuriyar Sarkin Musulmin Yarbawa sun tuna da ranar haihuwarsa a Ibadan

A ranar Asabar da ta wuce ne Zuriyar Sarkin Musulmin Yarbawa, marigayi Aare Musulmi Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao, suka gudanar da addu’o’i da bukukuwa, domin girmama wannan rana don cikarsa shekaru 70 da haihuwa. ‘Yan uwan marigayin da matansa da ‘ya’yansa da jikoki da tattaba kunne, su ne suka gudanar da wadannan addu’o’i, inda […]

Zuriyar Sarkin Musulmin Yarbawa sun tuna da ranar haihuwarsa a Ibadan
Zuriyar Sarkin Musulmin Yarbawa sun tuna da ranar haihuwarsa a Ibadan

A ranar Asabar da ta wuce ne Zuriyar Sarkin Musulmin Yarbawa, marigayi Aare Musulmi Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao, suka gudanar da addu’o’i da bukukuwa, domin girmama wannan rana don cikarsa shekaru 70 da haihuwa. ‘Yan uwan marigayin da matansa da ‘ya’yansa da jikoki da tattaba kunne, su ne suka gudanar da wadannan addu’o’i, inda babban Limamin Ibadan, Sheikh Busari Haruna ya jagoranci manyan malamai daga sassa daban-daban na jihohin Kudu maso Yamma wajen gudanarwa a cikin gidan marigayin da ke birnin Ibadan.

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, shi ne ya shugabanci zaman addu’o’in da wasu hamshakan ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da ‘yan boko da daruruwa talakawa maza da mata da suka saba samun taimako daga marigayin. Wannan taron dai shi ne irinsa na farko bayan rasuwar Aare Musulmi, Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao watanni takwas da wucewa.
A jawabinsa, Gwamna Abiola Ajimobi, ya bayar da sanarwar girmama sunan marigayi Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao, ta hanyar rada sunansa a kan sabuwar tagwayen hanyoyi ta Toll Gate zuwa Challenge da ke birnin Ibadan. Ya ce marigayin ya cancanci karramawa fiye da haka, saboda irin gudunmawarsa ga ci gaban jihar da kasa baki daya, tare da tallafa wa jama’a, musamman talakawa, ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. Gwamnan ya yi alkawarin daukar nauyin biyan kujerun Makka ga jama’a Musulmi domin karrama marigayin, wanda ya sadaukar da dukiyarsa wajen taimakon jama’a.
Sheikh Sulaiman Onikijipa shi ne ya jagoranci wasu manyan malamai wajen yin wa’azin tunatarwa da addu’o’in rokon Allah (TWT) ya gafarta wa marigayin. Mata biyu da marigayi ya bari a duniya, wato Hajiya Funso Alao da Hajiya Basirat Alao suna daga cikin mahalarta taron. Su ma manyan ‘ya’yan marigayin (mazaje) an gansu sanye da fararen hulunan habar kada da suturu iri daya, kamar yadda mahaifin nasu ya saba sanya suturu a lokacin da yake raye. Su kuwa tsofaffin mutane, maza da mata da suka saba zuwa gidan marigayin domin samun taimakon kudi da abinci da suture, su ma sun halarci wajen wannan addu’a cikin juyayi na rashin mai taimakawa.