Zuwa ga Masallata! (1)

Yau kuma tuna baya za mu sake yi, ma’ana mu sake maimaita wata wasika da na tsinta a bakin masallacin da muke salla a cikin unguwarmu, da kuma fatar sakon da ke cikin wasikar ya kasance mai amfani ga dukkan wadanda suka karanta wasikar ko kuma wadanda aka sanar da su abin da ta kunsa. […]

Zuwa ga Masallata! (1)
Zuwa ga Masallata! (1)

Yau kuma tuna baya za mu sake yi, ma’ana mu sake maimaita wata wasika da na tsinta a bakin masallacin da muke salla a cikin unguwarmu, da kuma fatar sakon da ke cikin wasikar ya kasance mai amfani ga dukkan wadanda suka karanta wasikar ko kuma wadanda aka sanar da su abin da ta kunsa. Mu sha karatu lafiya.
A shekarar da ta wuce ne, bayan mun gama sallar asham, a bakin masallacin da muke salla na tsaya ina neman takalmana, saboda dandazon jama’a; ga shi an dauke wutar lantarki, wato NEPA, na yi kicibis da wannan wasika. A lokacin da nake ta fafutikar neman takalmana, wasu bayin Allah sun taimaka mana, (mu da ba mu yi dabarar zuwa da cocila ba!) Wasu na haskawa da fitulun hannu, wasu kuma na kunna wayoyi domin mutane su samu damar ganin takalmansu. Ni dai sai kai-kawo nake yi, in duba nan, in sake dubawa can, domin kuwa a hannuna kafa daya ce, dayar kuwa ban sani ba ko an yi kutubal da ita ne! Can bayan kyauren masallaci na tsinto daya kafar takalmin nawa. Ina kokarin jefa kafa cikin takalmin sai na ji yatsuna na cin karo da wani abu da ba cikin takalmin yake ba. Na ja da baya na koma gindin dakalin masallaci, na sa hannu cikin takalmin sai na yi kicibis da wata farar takarda, ban ko damu na ga abin da ke ciki ba, na sa hannu na cire, amma maimakon na yi jifa da ita sai na rike a hannuna, na sa takalmana, na shura kafata, na isa gida.
Bayan na isa gidan ne, sai na kunna fitilar da ke kusa da gadona in ga me ke cikin wannan takarda, domin abin ya daure mani kai ta yadda wani zai sakala wannan takarda a cikin takalmina. Na jawo fitilar sosai kusa da takardar, domin ba na iya ganin rubutu sosai in ban kawo haske kusa da rubutu ba ko kuma na sa gilashin idona ba. Ina duba wannan takarda, sai na ga wasika ce daga MASALLACI zuwa ga MAHALARTA MASALLACIN da na fito. Abin ya ba ni mamaki! Na ce ta yaya masallaci zai rubuto wasika ko dai wasa ne yara suke yi ko kuma wani ya rubuta ya ajiye domin ya tsokane ni! Na dai daure na warware takardar da kyau na kuma karanta abin da ke ciki, abin da wasikar ta kunsa ya ba ni mamaki kwarai da gaske; amma domin kada na bata zancen, bari na amaye abin da masallacin ya ce da mahalartansa a cikin wannan wasika, domin Hausawa na cewa waka bakin mai ita ta fi dadi. Ga abin da wasikar ke cewa:
“Zuwa ga mahalarta wannan masallaci mai albarka. Yau babbar rana ce, domin kuwa an fara azumin watan ramadana, mai alfarma. Kuma na ji dadin ganin cewa kusan mako na biyu ke nan da kuke ta yi mini hidima. Ba ma ni kadai ba har sauran ’yan uwana masallatai, ba nan unguwar kurum ba, dukkan fadin jiha da kasa da ma duniya baki daya. Na san kuna yin haka ne domin wata mai albarka, watan AZUMIN RAMADAN ya kama. Lallai kun kyauta! Kun dai sa an yi mini fenti na koma sabo fil. Kun sa an yi mini bayan gida, ta yadda yanzu, ba sai kun bi bangaye kuna yi mini fitsari ba, balle kuma wasu daga cikinku da ke yin mini kashi a cikin harabata. Wannan abu ya yi mini dadi, na kuma gode kwarai da gaske. Haka da kuka sake kafet din da ke cikina, kuka maye ta da darduma shi ma ya faranta mini rai, abin ya yi mini dadi. Irin yadda na ga samari na ta didima, abin sai sam-barka! An cire tsofaffin kafet-kafet da suke ta faman wari, an baza mini sababbi ’yan Saudiyya ba ’yan China ba, ga fitilu sai haskaka ni suke tamkar wata dan daren sha biyu. Tubarkalla! A gaida wadannan masu sallah a cikina. Yadda kuma kuka sa aka yi man bohol, ruwan alwala na gudana a famfuna, wannan shi ma abin alfahari ne. Ga sabuwar lasifika! Ga kabod-kabod har guda biyu shakare da Al’kur’anai domin masu neman lada. Kai da ji da gani, ka san na zama dan gata, na zama dan lele! Kulawar da ta dace da ni ke nan da sauran ’yan uwana. Ba wannan kadai ba, yadda kuke ta faman kawo abincin buda baki kowace rana ta Allah; dabino, ruwan sha, kosai da kunu da dankali da ayaba da lemu da makamantansu domin ciyar da miskinai a cikina da kuma harabata, abin burgewa ne! Haka ma abincin dare da na sahur da kuke aika wa marasa shi, daga wannan lungu zuwa wancan sako, shi ma yana burge ni, shi ya sa ni ma nake kasancewa daga cikin masu taya ku addu’a, Allah ya biya!
To amma ina ganin ya dace in yi muku wannan bayani tun yanzu, ba girin-girin ba, ta yi mai. Ina fata wannan kwalliya da kuke ta yi mini. Wannan gyara da kuke ta faman yi mini. Wannan kamshi da kuke ta fesa mini. Wannan sadaka da kuke ta yi ga masu buda baki kowane watan ramadan a cikin kowace shekara. Wannan abinci da kuke ciyar da marasa galihu da shi a kullum rana ta Allah, ba don kawai saboda shigowar wannan wata mai alfarma na AZUMIN RAMADAN ba ne kuke yin haka!
 Za Mu Ci Gaba