Zuwa ga Masallata! (2)

Wannan gyara da kuke ta faman yi man. Wannan kanshi da kuke ta fesa man. Wannan sadaka da kuke ta yi ga masu buda baki kowane watan Ramadan a cikin kowace shekara. Wannan abinci da kuke ciyar da marasa galihu da shi a kullum rana ta Allah, ba don kawai saboda shigowar wannan wata mai […]

Zuwa ga Masallata! (2)
Zuwa ga Masallata! (2)

Wannan gyara da kuke ta faman yi man. Wannan kanshi da kuke ta fesa man. Wannan sadaka da kuke ta yi ga masu buda baki kowane watan Ramadan a cikin kowace shekara. Wannan abinci da kuke ciyar da marasa galihu da shi a kullum rana ta Allah, ba don kawai saboda shigowar wannan wata mai alfarma na AZUMIN RAMADAN ba ne kuke yin haka!
Ina kuma fata ba wai don lagwadar da ke jibge cikin goma na karshen wannan watan ba ne kuke yi man abin da kuke yi! In don shigowar wannan wata mai alfarma ne ko kuma don kawai ku ji dadin kwana cikina lokacin i’itikafi, kuna neman daren Lailatul kadari a cikin kwanakin nan masu zuwa, to sai in ce, an yi ba a yi ba ke nan!
Idan kun dage sake man rufin kwano da kafet da gina wurin ba-haya da yin sadaka dare da rana da faranta wa marasa galihu saboda watan AZUMI ya zo, amma bayan watan ya wuce, lasifikata ta lalace ku kasa gyarawa. Bohul dina ko rijiya ko kuma tankuna ko tukunyoyina na ajiyar ruwa su kasance ba ruwa tattare da su ko bohul ya bar kawo ruwa, ko rijiyar ta kafe ko a rasa masu zuba ruwa a tankunan ko tukunyoyin; ku yanzu sai ku yiwo alwala daga gidajenku, ku taho kuna takama,ku shigo ku yi Sallah a cikina, ku fice ba ku damu ba, to wannan shi ne badi ba rai.
Idan kuna yin abin da kuke yi a watan Ramadan ne kurum, amma daga baya in an yi ruwan sama, kwanona ya huje ruwa na zuba a cikina, ba mai gyarawa, har kafet ko darduma ko tabarmin da ke cikina su jike, sai wari nake yi, to zan ce ban ga amfanin wannan ibada taku ba! Ke nan da ma can taimakawa da kuka yi a gyara ni tun kafin bayyanar watan azumin Ramadan, ba don Allah kuka yi ba. Ku sani in kun yi wa kanku karya, shi Mai-duka ba wanda ya isa ya yi maSa karya, Yana kallonku, Ranar Tashin kiyama kuma na ga yadda za ku iya amsa maSa tambayar nan ta man Rabbuka….
‘Idan ba ku sani ba to ku kara sani, ku kuma bude kunnuwanku ku ji ni da kyau! Idan dai a cikin wannan wata mai alfarma, za ku ciyar da marasa galihu daga dukiyarku domin neman alfarmar da ke tattare da watan RAMADAN ne kurum, sauran al’amurran rayuwar yau da kullum da Mai-duka ya dora muku ku yi watsi da su, da ana ba ku shawara ku dauka, da sai na ce kada ku ci gaba da wahalar da kanku! Na ce haka ne domin raina na kuna a duk lokacin da na ga marasa galihu sun shigo cikina, ko su yi tsaye a harabata ko kuma kun kore su can bakin titi nesa da ni bayan watan Ramadan ya wuce, suna kuka, cikin tufafin da kai ba ka iya sayen su kwabo, datti ya yi musu katutu, sa’annan uwa-uba suna  rokon a taimaka masu da abin da za su ci da iyalinsu. Idan har za ku bar talakawa, fakirai, miskinai su ci gaba da yin barar abinci da tufafi da kudin haya da na sauran kayan masarufi bayan watan Ramadan ya wuce, sai ni kuma in tambaye ku, ina zuciyarku ta taimako ta tafi bayan wucewar watan Ramadan? Tana ina?
Ku sani duk abin da kuke yi a cikina a kowane watan Ramadan ina sane; sai dai ina son ku fahimci wani abu, shi wanda ya gyara ai ya sani, wanda kuma ya bata, ai ya sani. Shin falalar Ramadan ce ke sa ku yin abin da Mai-duka Ya ce? Shin idan da ba watan azumin Ramadan, shi talaka ko fakiri ko miskini bai da katabus ke nan? A matsayina na wanda kuke bauta a cikina kowace rana ta Allah, ku sani na san irin addu’o’in da kuke faman yi a cikina. Wasu daga cikinku har kuka kuke yi wa Allah domin Ya biya muku bukatunku. A duk lokacin da na ga kun gama Sallar Tarawihi ko kuma kun dage sallolin dare cikin takawa da damuwa da daga kokon bararku zuwa ga Allah, a cikina ko harabata, sai na ji wani wasi-wasi na ratsa mani rayuwata. Shin idan har Mai-duka Ya amsa muku daga cikin addu’o’inku da nake ji kuna yi kullum a cikin wannan wata mai alfarma, ku kuma me za ku saka wa talakawanSa da shi a cikin watan ko bayan watan ya gushe? Na san dai Mai-duka ba Ya bukatar wani abu daga gare ku, domin Shi Wadatacce ne kuma Yalwatacce, amma ku kuma me za ku yi ku nuna cewa kun gode maSa da wannan ni’ima da Ya yi muku?
Ina jin wasu daga cikinku a cikin talatainin dare kuna neman a kara muku daga cikin dukiyar da kuke da ita. Idan na kalle ku lokacin da kuke mika wannan  koke sai na ce to wai me kuke bukata kuma? Tufafin da wasunku ke sanye da  su a lokacin rokon Allah a cikina, za su sayi tufafi 100 na wasu miskinai da ke cikin masallacin tare da ku, kun dage a kara muku, amma me za ku yi da su idan har Allah Ya biya muku bukatunku? Wannan shi ne ke damuna! Idan har Allah Ya amsa muku saboda darajar wannan wata mai alfarma, to ya kamata ku yi wani abin a-zo-a-gani daga cikin wannan rabauta da Ya yi muku.
Za mu ci gaba