Zuwa ga masu dinkin zamani

Gaisuwa da fatan alheri zuwa ilahirin musulman Duniya kwata, da fatan Allah ya karba mana ibadunmu, yasa muna daga cikin ‘yantattun bayi. A bisa la’akari da wannan lokaci da muke ciki na karasowar Sallah, nake amfani da wannan dama domin inyi kira zuwa ga ‘yan uwa, madinka, masu sana’ar dinkin mata. Hakika tarbiyya babban abu […]

Zuwa ga masu dinkin zamani
Zuwa ga masu dinkin zamani

Gaisuwa da fatan alheri zuwa ilahirin musulman Duniya kwata, da fatan Allah ya karba mana ibadunmu, yasa muna daga cikin ‘yantattun bayi. A bisa la’akari da wannan lokaci da muke ciki na karasowar Sallah, nake amfani da wannan dama domin inyi kira zuwa ga ‘yan uwa, madinka, masu sana’ar dinkin mata. Hakika tarbiyya babban abu ne wanda iyaye suke matukar shan walahar gaske kafin gina ‘ya’yansu da ingantacciyar tarbiyya domin su tashi mutanen kirki abun alfahari cikin al’umma. Tabbas wasu daga cikin telolin wannan zamani suna taka muhimmiyar rawa wajen lalata tarbiyar ‘ya’ya mata, ta hanyar yimusu dinkunan zamani na fitsara wanda yake nuna tsiraici kai tsaye, kuma wannan haramun ne a cikin addinin musulunci, kuma yaci Karo da al’adar malam Bahaushe.

Idan mukayi waiwaye a da can kafin zuwan wannan zamani da muka shagala da bin al’adar yahudawa, ansan malam bahaushe da shiga da kyautata yanayin suturarsa abin sha’awa da iya kyakkyawar mu’amala da mutanen da ba jinsin kabilarsa ba, Sannan ga natsuwa da kamun Kai da dattako a duk inda ya tsinci kansa, a bisa wannan duk inda bahaushe ya shiga a cikin al’ummomi daban-daban shigarsa da al’adarsa ta kan banbanta da sauran wasu Mutane da al’adunsu ba daya ba. Amma yanzu zamani ya zo mana da wani Abu daban Wanda yake kokarin yin hannun Riga da al’adunmu da dabi’unmu. wallahi masifar zamani babu inda zata kaimu sai danasani da tarin nadama.

Shin ko zai kasance ibadar azumin wata guda cur mu wancakalar da shi a cikin wuni daya ko biyu bayan azumi? Babu ko shakka wannan bai kyautu ba, ya kamata muyi duk mai yiwuwa domin tsira da kima da mutuncinmu, in har munason mu samu babban rabo, wajibine mu kaucewa abubuwan asha, da yada barna a cikin al’umma.

Duk abinda idon aka yiwa ‘yar ka ko ko kanwarka ko ‘yar uwarka bazakaji dadi ba, to lallai bai kamata a sameka da hannu dumu-dumu wajen yiwa ‘ya’yan wadansu ba, Domin Allah madaukakin sarki zai tambaye mu duk abinda muka aikata na alheri ko akasin haka.

Ya ku ‘yan uwa masu sana’ar Dinki! Idon kuka hada kanku kuka kyamaci yin dinkin fitar da tsiraici, insha Allahu wannan zai matukar tasiri wajen rage yin shigar banza a cikin al’ummarmu.

A karshe muna rokon Allah ya samu daga cikin ‘yantattun bayinsa wannan wata mai falala da albarka da rahama, muna fatan Allah ya zaunar mana da kasarmu lafiya da kwanciyar hankali da wadata.

Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau jihar Zamfara 08133376020