Zuwa ga masu sayar da katin zabensu
Yanzu haka dai kasuwar sayar da kuri’a ta fara kankama, kasancewar zabubbukan Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa na kara fuskanto mu, wannan kasuwa dai ba bakuwa ba ce a tarihin siyasar Najeriya, inda al’umma suka kasance cikin duhun kai na fahimtar muhimmancin katin zabe da kuma shi kansa zaben.An sha ruwaito matasa […]
Yanzu haka dai kasuwar sayar da kuri’a ta fara kankama, kasancewar zabubbukan Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa na kara fuskanto mu, wannan kasuwa dai ba bakuwa ba ce a tarihin siyasar Najeriya, inda al’umma suka kasance cikin duhun kai na fahimtar muhimmancin katin zabe da kuma shi kansa zaben.An sha ruwaito matasa suna sanya ganye a kawunansu (alamar su na sayarwa ne), kazalika rahotanni sun tabbatar da yadda baragurbin ’yan siyasa suke amfani da kayan masarufi irin su shinkafa da taliyar indomie da sabulun wanka da atamfa da sauran kayan amfanin yau da kullum don farauto masu jefa kuri’a su zabe su.Wani abin da ya kara tabbatar da karancin wayewar kan wadansu masu zabe shi ne labarin wata cibiyar zabe da na ji daga bakin fitaccen malamin tarihin nan na Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa da ke Katsina Dokta Aliyu Muhammad Muri inda yake labarta min yadda aka dora tukunya a wannan rumfar zabe aka dafa shinkafa da wake ga duk wanda ya zabi jam’iyyar da ta girka wannan abinci za a zuba masa ya ci. Wannan ya faru ne a cikin Jihar Katsina a zabubbukan da aka yi a baya.
Misalan abubuwan takaici da sayar da ’yanci da suka faru a zabubbukan da suka gabata tun daga 1999 zuwa yanzu suna da yawan gaske wadanda yanayi ba zai ba ni damar jero su ba. Wadannan misalai da na gindayo a matashiyar wannan makala sanannu ne a harkar zaben Najeriya, sai dai an yi ta samun bambancin ra’ayi a tsakanin masu fashin baki a kan lamuran yau da kullum da kuma sauran gama-garin mutane. Wadansu suna danganta wannan da talaucin da ya yi wa al’ummar Najeriya kanta, wannan ne yake haifar da hakan, wadansu masu matsakaicin ra’ayi sun karfafa gwiwar duk wanda aka kawo wa irin wannan toshiyar baki ya karba ya yi shiru da bakinsa in ya je wajen dangwalawa ya dangwala wa wanda ya dace.Wadanda suka tsawaita kuwa suka ce ai duk wanda ya ce ka sayar masa da kuri’a to raina wayonka ya yi don haka ka yi watsi da wannan tayi, wannan mahangar masu fashin baki ke nan.
Kafin mu nutsa sosai ya kamata mu sake kallon mene ne tasirin kuri’a? Kuri’a wani makami ne da talaka yake amfani da shi wajen zabar wa kasarsu shugabannin da za su mulke shi tsawon wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanada.Kuri’a tana da tasiri sosai wajen tantance dan kasa nagari da baragurbi, a takaice dai kuri’a tana da tasirin gaske ga rayuwar talaka.
Bisa la’akari da wannan za mu ga cewa ashe kuri’a ba hajar kasuwanci ba ce. Idan muka yi la’akari da muhimmancin kuri’a za mu fahimci cewa za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen zaben wanda zai ceto tattalin arzikinmu har mu fita daga kangin talaucin da ake hasashen shi ne ya jefa mu a kazamar kasuwar sayar da ’yanci.
Ba shakka wanda aka haifa mara hankali, ya yi hankali, ya fi wanda aka haifa da hankali, hankali da kuma natsuwa. Idan muka dubi inda kwadayinmu da son kanmu ya kai mu sakamakon sayar da ’yancinmu a ranakun zabe ya ishe mu darasi wajen kaurace wa komawa ’yar gidan jiya, anya kuwa muna tuna wa kanmu cewa idan muka dangwala wa mutumin kirki ya ci ya yi abin kirki muna da kamasho a cikin sakamakon da zai samu a nan duniya da Lahira? Shin muna tuna cewa idan muka biye wa ’yan kudaden da ba za su kashe mana kishirwa ba muka zabi baragurbin shugaba shi ma muna da namu kamashon? Shin muna tuna makomar ’ya’yanmu da kannenmu da jikoki kafin mu yi zabe, ko buhun shinkafar da Honorabul ya biyo dare ya kawo mana muke tunawa?
Muna tuna yadda shugaba yake nunawa tsakanin ’ya’yansa da na talaka ko kuwa turamen atamfa ’yar soso sun rufe mana ido? Lokaci ya yi da za mu hadiye kwadayinmu wajen juya wa duk wata hulda da ta danganci sayar da kuri’a, mu yi wa kanmu kiyamullaili mu zabi shugabannin da za su kai kasarmu tudun-mun-tsira ko sun ba mu kudi ko ba su ba mu ba.Talauci fa ba hauka ba ne don haka mu zurfafa tunanimu sosai wajen wannan zabe mu tsare abin da muka zaba kada mu yi baya-ba-zane.Mu tabbatar an yi mana adalci, mu sani duk abin da zaman lafiya bai ba mu shi ba, tashin hankali ba ya ba da shi.Don haka mu zama jakadun zaman lafiya a duk inda muka samu kanmu.
Kwamared Sagir Musbahu Daura Dole
Za a iya samunsa a 08095597525