Zuwa ga Sanusi Lamido Sanusi (1)
Mai martaba na san kila ka manta yawancin abubuwan da ka kattaba a jaridu da dadewa a baya, amma kila ba ka manta da wannan rubutun da ka yi ba a shekarar 2001, mai taken ‘The Adulteress’ Diary’, inda cikin shagube da wasa da harshe ka yi kira ga mai karatu da ya yi maka […]
Mai martaba na san kila ka manta yawancin abubuwan da ka kattaba a jaridu da dadewa a baya, amma kila ba ka manta da wannan rubutun da ka yi ba a shekarar 2001, mai taken ‘The Adulteress’ Diary’, inda cikin shagube da wasa da harshe ka yi kira ga mai karatu da ya yi maka aikin gafara game da gautsin harshen da ka yi amfani da shi, amma kuma a yi aiki da darussan da ke kimshe a cikin rubutun. Ni dai ban manta ba Mai martaba, musamman inda kake cewa ka yi wancan rubutun ne domin duniya ta fahimci irin rashin adalcin da ’maza’ suke yi wa mata irin su Safiya Hussaini Tungar Magaji ta hanyar fakewa da addinin Musulunci ko kuma Shari’a. Ka nuna rashin jin dadinka kan yanke wa Safiya Hussaini hukuncin kisa saboda ta haihu ba tare da an yi mata aure ba, hukuncin da ‘maza’ ne suka yanke shi ga ‘mace’ marar gata. Wannan ba daidai ba ne kamar yadda ka nuna. Ka nuna ’yan Hisba da malaman addini da ke ta farautar Safiya da kuma ke ta wa’azin ta mika wuya shari’a ta hau kanta a wancan lokaci, ba su yi mata adalci ba, domin sun yi haka ne a matsayin ‘maza’ ba masu yin adalci ba.
Tun a wancan lokaci na fahimci cewa fahimtarka daban da ta sauran ’yan boko da kuma saraki ko malamai da ka gada ko ka yi kurme a ciki. Na ji dadin bayanin da ka yi na cewa ‘al’ummarmu ta kasance tamkar dankali mai sankara ce, ta lalace ta kowace hanya.’ Ka yi nuni da cewa al’ummarmu ta kasance tamkar wadda ke rayuwa a zamanin Yahudawan dauri, ba abin da aka sa gaba sai aikata zina, kuma wai yawancin laifuffuka irin wadannan, kamar yadda ka nuna ‘mata’ ne ke haddasa su. Ka dai nuna cewa za ka iya yarda da wannan hasashe, cewa maza ba su da laifi wajen aikata zina, sai mata, amma tambayar da ka yi game da sauran lamura ita ce ta burge ni. Inda kake tambayar idan har mata ne ke sa maza aikata zina, to wa ke sa mazan aikata laifuffukan luwadi, inda maza ke neman maza? Ke nan kamar yadda ka bayyana, mazan ma ba baya ba ne a barna irin wannan.
Wannan ya sa a wanncan lokaci nake bibiyar rubutunka domin na fahimci wani abu game da kai, manazarcin al’umma ne da matsalolinta da hanyoyin da za a bi a yi maganin wadannan matsaloli. Kamar yadda ka bayyana a wancan lokaci, yawancin matan Hausawa suna cikin tsaka-mai-wuya ce, musamman ganin cewa malamai sun aza musu rigar tsana da suke cewa ba su da ilimin addini ga su kuma wawaye! Yadda ka bayyana rashin fahimtar malamai da al’ummar kasar Hausa a lokacin na gane cewa ba da ka kawai kake zance ba, sai ka auna, sai ka girgiza kaza, ka ji mai kwai a ciki, kake saye. Shi ya sa ban yi mamaki ba da ka ce, ko da an kashe Safiya Husaini, ba abin da zai canja a kasar Hausa, domin ba za mu dawo da rayuwa irin ta zamanin Dan Fodiyo ba ko kuma Hausawa su bar tafka barna da rashin adalci ba. Daga irin naka tunanin na kara assasawa da gina nawa tunanin daga baya a rayuwa. Domin kamar yadda kake cewa, kashe Safiya ba zai hana cin hanci da sata da almundahana ba a fadojin Gwamnatin Tarayya ko jihohi ko kananan hukumomi ko a ofisoshin kamfanoni da bankuna ba, wallahi na yarda da wannan hasashe. Yadda ka kalubalanci shugabannin wancan lokaci su fahimci gaskiya da aiki da ita, abu ne da ya yi min tasiri a rayuwa.
Ka ce idan har masu son tabbatar da Shari’a da gaske suke yi to don Allah su rantse da Kur’ani cewa ba su taba aikata zina a rayuwarsu ba. Yadda ka nuna wa shugabannin wancan zamani cewa munafunci bai yi ba a rayuwa, ya shere ni ya Mai martaba!
Idan ba ka manta ba, wancan kalubale ba ga malamai kadai ka jefa shi ba, ka hada da ’yan siyasa da sarakuna da makamatansu! Wannan yaki da kai da wadansu irinka suka yi ya taimaka wajen ceto ran ’yar baiwar Allah, Safiya Hussaini, ya kuma wayar da kan mafi yawancin matasa, irina da wadansu masu sauran rabo daga cikin shugabanni.
Sai dai Mai martaba, tun a wancan lokaci na san za a yi daga da kai, kuma wani abu makamancin abubuwan da suka faru da kai a rayuwa, kama daga zamanka Gwamnan Babban Bankin Najeriya da Sarkin Kano, tamkar majigi ne da aka nuna min a cikin kundun raina, kaddara ce ta riga fata!
Za mu ci gaba