Zuwa ga Wadari!
Assalamu alaikum, ina yi maka fatar alheri Malam Ibrahim Malumfashi. Hakika ni ma’abocin karanta shafinka ne a jaridar Aminiya, kuma ina fahimta tare da karuwa da rubutunka na kowane mako, Tabbas duk da cewa ban san ka ba idan ba ta shafin ba, amma na fahimce ka kwarai da gaske, duk wanda ke da aniyar […]
Assalamu alaikum, ina yi maka fatar alheri Malam Ibrahim Malumfashi.
Hakika ni ma’abocin karanta shafinka ne a jaridar Aminiya, kuma ina fahimta tare da karuwa da rubutunka na kowane mako, Tabbas duk da cewa ban san ka ba idan ba ta shafin ba, amma na fahimce ka kwarai da gaske, duk wanda ke da aniyar ganin mulkin adalci mai kishin kasa da zarar ya duba shafin zai fa’idantu.
Idan har ba wata cikas, ina so wata rana ka ba ni damar yin rubutu kan maudu’in (Arewa ba arziki ne?) ko kuma (’Yan Arewa mu tashi tsaye) a wannan shafi naka, ka kuma sanar dani ka’idojin da ya dace na san su a kan shafin.
Da fatar zan samu gamsashshiyar amsa daga gare ka. Na gode
Usman bin Affan Damaturu, Sakataren kungiyar Zabi Sonka, reshen karamar Hukumar Damaturu Jihar Yobe, kuma jami’i a kungiyar Muryar Talaka, Damaturu. 08038001563
-Malam Usman na gode da bibiyar WAdARI, shafin nawa ne, amma duk mai wani ra’ayi da yake son mu karu da shi yana iya turowa, in ya yi ma’ana za mu buga Insha Allah.
Daga Ahmed Baba Ahmed
Lallai mun shiga makaranta game da rubutun da ka yi kan BUHARI, Allah Ya kara basira.Tsokacin da zan yi a tawa fahimtar talakawa ne kawai suke bukatar canji, shi kuma canji yana faruwa ne ta bangarori guda biyu; hanyar amfani da kuri’a wato zabe da tarzoma, wato zanga-zanga kamar yadda ya faru a wasu kasashe. Ta bangaren masu mulki sun yi nasara wajen raba kan talakawa da bambancin addini da kabilanci, don haka talakawa wannan bambance-bambance ne babban kalubale da yake hana su iya kawo canjin da ake bukata. Har ila yau akwai masu ruwa da tsaki wadanda ake kira ‘stakeholders’ ko kuma ‘cabals’ masu dora mutane a kan madafun iko suna juya su daga gefe, wannan lalura ita ma tana hana canji domin masu rike da mulki na dibar dukiyar kasa suna kashe-mu-raba-da-su.
Cikas da da talaka ke samu wajen kawo canji shi ne kuri’arsa tana aiki kasa da kashi 35 cikin 100 ne. Na biyu babu wanda zai jagorance shi cikin shugabanni wajen gangamin neman canji, don haka shi talakan Arewa, musamman Musulmi ya mika wuya ga Buhari.
Ta bangaren Buhari kuwa lallai ba shi ba ne kadai ke iya kawo canji ta bangaren zabe, amma shi kadai ne wanda ya bayyana zahiri a fili wanda talakan Arewa ya gamsu da shi, yunkurin kawar da shi daga takara na iya karya gwiwar masu zabe daga yankin Arewa ganin shi Buhari ya fi sauran da suka bayyana kansu yawan magoya baya daga yankin Arewa, don haka nake ganin mu dubi matsalolinsa wadanda suka hada da rashin karbuwa daga Kudancin Najeriya ko rashin karbuwa daga Kiristocin Arewa. Sai magoya bayansa ire-iren kalaman da suke yi a fili, misali, sai Buhari! Sai mai Sallah! Ban da arne da sauran su, sai mu duba shin wannan karon idan aka tsayar da Buhari takara karkashin jam’iyar adawa ta APC ana iya kauce wa matsalolin, kuma ana iya samun nasara? Idan gyara za a yi daga kamfen din sai a yi, idan kuma ba shi yiyuwa, to za a koma gidan jiya. Don haka sai a duba a maye gurbinsa da wani wanda muke kyautata masa zaton zai samu karbuwa, kuma yana da dama-dama wajen hana rashawa da tabbatar da adalci.
Ta bangaren gyara kuwa duk da yake akwai bambance-bambance kamar yadda ka kawo cewa akwai bangaren zartarwa wato masu mulki da na majalisa da bangaren shari’a kuma duka sai an hada hannu kafin a kawo canjin da ake bukata, lallai haka ne amma ai sai da shugaba kafin ya hada kan sauran, idan sama ta yi kyau kasa sahu za su bi.
Zan koma da baya na yi batun masu mulki da shugabannin al’umma wadanda na ce a baya su ba su bukatar canji, kasancewa suna tatsa daga dukiyar kasa, ba za su bari canji ya samu ba, sai talakawa sun yake su ta hanyar kyamatarsu da dukiyarsu, mu daina kwadayi.
A karshe nake ganin 2015 idan canji da muke bukata bai samu ba, to lallai canji zai zo ne kawai ta bangaren jam’iyyar adawa, su umarci talakawa su yi gangami wajen neman rushe wannan gwamnati ta hanyar zanga-zanga domin ba na ganin canji zai samu a cikin jJam’iyyar PDP, kasancewa jam’iyyar ba za ta taba dora mutanen kirki a kan madafun iko ba, idan muka yi la’akari da tsarin jam’iyyar da irin mutanen da ke juya ta.
Haka kuma masoya Buhari su gane ita siyasa ’yar lallami da dabara ce don haka idan ana so ya yi nasara sai an tafi da kowa da kowa kuma ana bukatar kuri’a ta kowa da kowa, don haka akwai bukatar wayar wa jama’a da kai musamman wadanda ba sa son sa, ’yan Kudu da Kiristocin Arewa a nemi goyon bayansu, mu gane kuri’unmu na Arewa kawai ba za su sa Buhari ya ci zabe ba.
Allah Ya taimake mu da kasarmu, Allah Ya kawo mana canji nagari, Allah Ya yi mana jagora.
Daga Jamilu Sabi’u
Lallai gafarta Malam, maganarka dutse ce. Annabin Rahama Muhammad Mai tsira da amincin Allah sun dawo yaki, ga shi an ji jiki, maza sun jikkata, ana ta fama da raunuka. Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai suka ji ya ce “Raja’ana minal jihadil asgar ila jihadil akbar,” wato “Mun dawo daga karamin yaki zuwa ga yaki mafi girma ko mafi wahala.” Sahabbai (Allah Ya yarda da su) cikin mamaki suka tambayi Manzon (SAW) wane yaki ne mafi girma daga wannan? Sai ya ce “Jihadin NAFS ‘ wato yakar ZUCIYA. Ma’ana soye-soyen zuciyar.
Zuciya kullum tana umarni da mummuna. Don haka sai an ladabtar da ita a kan dabi’o’i madaukaka, hakan zai haifar da al’umma tagari masu kishin kasa da al’umma, wadanda za su ciyar da kasa gaba. Allah Ya daidaita al’amuranmu, Ya taimake mu, amin.
Daga Darda’u Idris Safana
Na tabbata duk wanda ya kai shekara 10 zuwa sama da haka zai gaskanta abin da Malam ya fada kuma babu ko shakka haka yake. To abin tambaya a nan Buhari daga wace kasa ya zo? A ina aka haife shi? A ina ya yi yarintarsa har ya girma? Ina ya yi karatu? Su wa suka ba shi tarbiyya? A ina ya yi aiki har aka ga kyawawan halayensa? Amsar dai guda daya ce, wato Nijeriya. Idan kuwa haka ne, da ni da kai da ke da ita me zai hana mu yi koyi da irin kyawawan halayen Buhari da duk muka amince yana da su. Wani abu da muka mance shi ne mu ji tsoron Allah mu kyautata al’amuranmu na yau da kullum tsakaninmu da duk wanda Allah Ya hada mu da su. Mu kuma kiyaye dokokin Allah ta hanyar yin abin da Ya umarce mu da barin abin da Ya hane mu, mu ga in abubuwa ba su canja ba. Lallai Allah (SWT) ba Ya canza wa mutane ni’ima har sai sun canja da kansu. Ma’ana da mutane sun bar dokokin Allah, to, sai masifu su yi ta faruwa a cikin al’umma. Kuma ana ba al’umma shugaba daidai da irin halayensu. Matukar ba mu gyara halayenmu ba, haka za mu kasance a kullum. Allah Ya shiryar da mu.
Zuwa ga Wadari!