Zuwa yanzu ba wani dalilin da zai sa a sake dage zabe

A ranar Juma`a 6 ga watan Fabrairun da ya gabata Hedkwatar Rundunar tsaron kasar nan, ta hannun babban Hafsaf Hafsoshin Dakarun kasar nan Cif Air Marshall Aled Badeh suka fito karara suka shawarci Hukumar zabe mai zaman kan ta kasa wato INEC, da lallai ta dage zabubbukan kasar nan da makonni shidda, wadanda a wancan […]

Zuwa yanzu ba wani dalilin da zai sa a sake dage zabe
Zuwa yanzu ba wani dalilin da zai sa a sake dage zabe

A ranar Juma`a 6 ga watan Fabrairun da ya gabata Hedkwatar Rundunar tsaron kasar nan, ta hannun babban Hafsaf Hafsoshin Dakarun kasar nan Cif Air Marshall Aled Badeh suka fito karara suka shawarci Hukumar zabe mai zaman kan ta kasa wato INEC, da lallai ta dage zabubbukan kasar nan da makonni shidda, wadanda a wancan lokacin ta shirya gudanarwa aranaikun 14 da 28 ga watan na Fabrairun. Babban hamzarin da Hedkwatar tsaron ta bayar a wanncan lokacin, shi ne ba za a samu sojojin da za su ba da kariyar tsaro a cikin aikin gudanar da zabubbukan ba, (a lokacin Kotun daukaka kara ta Kaduna ba ta yanke hukuncin cewa sojoji ba su da ikon ba da kariya a cikin zabubbukan kasar nan) don kuwa a fadarta, Dakarunta za su kasance filin daga a shiyyar Arewa maso Yamma don yakar `yan kungiyar Jama`atu Ahlis Sunnah Lid Da`awati Wal jihad, da aka fi sa ni da Boko Haram, wato a jihohin Barno da Yobe da Adamawa, shiyyar da `yan kungiyar suka kai fagen kafa Daularsu, a cikin kusan shekaru shidda da suka fara wannan gwagwarmaya.

A wancan lokacin`yan kungiyar, sun kama kananan Hukumomi sama da 20 daga wadancan jihohi uku, 15 daga jihar Barno, inda nan ne asalin inda gwagwarmayar `yan kungiyar ta samo asali tun a shekarar 2009. Wasu daga cikin kananan Hukumomin da `yan kungiyar suka kama sun hada da Gwoza da Bama da Damasak da Abadam da Malam Fatori da Marte da Mafa da Kukawa da Monguno da Gomburu da dai sauransu. A Jihar Yobe kuwa sun yi nasarar kame Hedkwatocin kananan Hukumomi uku da suka hada da Gujba da Gulani, ya yin da jihar Adamawa suka kiama Hekwatocin kananan Hukumomi irin su Mubi da Madagali.
Wani hamzarin lalle sai Hukumar ta INEC ta dage zaben da ya bayyana a wancan lokaci daga Ofishin shugaban kasa da itakanta jam`iyyar PDO mai mulki da gwamnatin tsakiya da sauran `yan kazaginsu shi ne kasa kammala rabon katin zabe na din-din-din. A wancan lokacin an kiyasata cewa daga cikin kusan masu kada kuri`a miliyan 68, da aka yi wa rijistar, mutane miliyan 24, ba su samu amsar katuttukan nasu ba, abinda ake ganin yin zaben a wancan lokacin zai iya haramtawa irin wadancan `yan kasa `yancin da suke da shi na zabar wanda ransu ya kwanta masu kamar yadda tanade-tanaden Kundintsarin mulkin kasar nan da na dokokin zabe suka tanada.
Wannan dagawa da aka yi da kuma irin yadda gwamnatin tarayya da ita kanta Hukumar INEC suka dukufa ka-in-da-na`in cikin gudanar da ayyaukan su ka iya ce Alhamdulillah! Idan har komai yana tafiya kamar yadda ake yanzu, to, kuwa ba wani dalili da zai sa a kuma sake bada shelar dage zabubbukan. Alal misali daga irin gumurzun da ake wajen kwato yankunan da `yan Boko Haram suka kwace zuwa yanzu dukkan Hedkwatocin kananan Hukumomi da garuruwa da kauyuka da ke kewayensua jihar Adamawa, sun riga sun dawo hannun gwamnatin tarayya kamar yadda aka ji Kakakin Hedkwatar tsaro, Manjo Janar Christ Olukolade yana fadawa manema labarai a jihar ta Adamawa a cikin wani rangadin gani da ido da wasu manyan Hafsoshin Dakarun kasar nan suka kai a yankunan da aka kwato din cewa “Zuwa yanzu ba sauran wani yanki da ke hannun Boko Haram din a cikin jihar ta Adamawa, Madagali dama shi ne gari na karshe, shi din ma ga shi yanzu an kwato shi.” In ji Kakakin Hekwatar Rundunar tsaron.
Inda har yanzu ake neman kwatowa ita ce Gwoza Hedkwatar karamar Hukumar Gwoza da ke cikin jihar Barno, wadda nan `yan Boko Haram din suka kafa Daular su tun a shekarar bara, ita din ma rahotanni zuwa yanzu sun tabbatar da cewa Dakarun hadin guiwar na kasashe Janhuriyar Nijar da Chadi da Kamaru da janhuriyar Benin da askarawan kasar nan suna can suna gwabzawa, don kwato ta (ba mamaki a lokacin da mai karatu yake karanta wannan makala, labari ya bazu akan an kwato Gwoza din). Ganin irin nasarar da ake samu a cikin wannan fada, ta sanya shi kansa Cif Air Marshall Badeh a wata ganawa da ya yi da manema labarai a makon da ya gabata, yake ba da tabbacin cewa “Har abada ba wani yanki na kasar nan da zai kara fadawa hannun `yan gwagwarmayar.” Anan sai mu ce Allahumma amin. Don kuwa ai ba wanda ya taba tsammanin hakan za ta taba faruwa, barec a dauki tsawon kusan shekaru shidda ba a kawo karshen annobar ba.
Koda yake har yanzu wasu daga cikin mutanen da waccan annoba ta raba da garuruwansu da gidajensu da ma harkokin rayuwarsu na yau da kullum su kusan miliyan 3, basu koma garuruwan na su ba, walau ko dai don fargaba da jimamin yadda za su taras da garuruwan nasu da yaki ya dai-daita, koma jimamin yadda zai ci gaba da kasancewa akan ba iyayensu ko mazajensu ko `ya`yansu koma `yan uwa da makwabta da sauran abokan zama, da kuma irin yadda za su gyara matsugunnansu da annobar ta lalata, wadda kuma ake kiyashin mutane sama da dubu 13,000, suka rasa rayukansu, baya ga wadanda suka jikkata, amma dai ko ba kome mafi yawansu rahotanni tabbatar da sun karbi katuttukansu na din-din-din na kada kuri`a.
Idan ka dawo akan katunan din-din-din na kada kuri`a kuwa, wadanda su ma kasa raba su ya sanya a ce a dage zabubbukan, zuwa yanzu Kakakin shugaban Hukuamar zaben Mista Kayode Idowu ya fadawa wani taron manema a Abuja a cikin makon jiya cewa zuwa ranar 12 ga wannan watan, aikin rabon katututtun kada kuri`un na din-din-din ya kai kashi 81.2 cikin 100, a kasa baki daya, inda ya kara da cewa jihohi 10, watoAkwa Ibom da Jigawa da Kebbi da Katsina da Sakkwato da Kaduna da Taraba da Zamfara da Gwambe da Imo, rabon ya kai sama da kashi 90 cikin 100. Jihohi takwas kuwa in ji Mista Idowu, wato Bauchi da Enugu da Kuros Riba da Kano da Anambara da Ribas da babban birnin tarayya Abuja, jama`arsu sun karbi sama da kashi 80 cikin 100, jihar Ogun ce ke baya da kashi 49.4 cikin 100. Ana fata tunda aikin rabon katuttukan zai kai har 22 ga wannan watan, to kuwa a samu akalla kashi 80 zuwa abinda ya yi sama na mutanen da za su karbi katuttukan nasu kafin cikar wa`adin.
Gwajin yin amfani da katin zabe na din-din-din da akai a wasu jihohi 12 na kasar nan wanda na yi bayanin nasarorinsa da ya samu a wannan shafi a baya, da kuma irin taron da Hukumar ta INEC ta yi da wasu masu ruwa da tsakiya akan zabubbukan a farkon wannan makon inda ta fayyace masu irin shirye-shiryen da take kai don giudanar da wadannan zabubbuka a ranaikun 28 ga wannan watan na Maris da kuma 11 ga watan Afrilu maizuwa cikin kamanta gaskiya da adalci, duk suna nuni da basauran wasu hujjoji da walau Askarawan kasar nan ko na jam`iyyar PDP, za su kara kawowa `yan kasa akan a dage zabubbukan masu zuwa, ko a ce za a kafa gwamnatin rikon kwarya, bare a ce kar a yi amfani da Na`urar tantance katin zabe. Don haka zabe kawai. Allah kuma Ya sa a yi lafiya.