Zuwan Buhari Amurka alheri ne ga Najeriya – Idi Zamfare
Wani tsohon dan siyasa Alhaji Idi Zamfare ya bayyana cewa ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Amurka ba karamin alheri ba ne ga Najeriya. Alhaji Idi Zamfare wanda daya ne daga cikin aminan Shugaba Buhari ya ce, “Ina da tabbacin cewa, abin da Buhari ya yi a Amurka ba zai taba yarda da duk abin […]
Wani tsohon dan siyasa Alhaji Idi Zamfare ya bayyana cewa ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Amurka ba karamin alheri ba ne ga Najeriya.
Alhaji Idi Zamfare wanda daya ne daga cikin aminan Shugaba Buhari ya ce, “Ina da tabbacin cewa, abin da Buhari ya yi a Amurka ba zai taba yarda da duk abin da zai cutar da kasar nan ko al’ummarta ba. Mu lura da irin mutanen da ya dauka zuwa Amurka wace kabila ce daga cikin manyan kabilun kasar nan da ba sa cikin tawagar?”
Zamfare ya ce, “Buhari mutum ne mai riko da addini wanda kuma yake martaba na wasu. Amma abin da zan tunatar da jama’a shi ne, kada su manta an yi masa wannan gayyata ce a cikin watan azumi wanda a nasu tsarin tun a wancan lokaci suka so ya je amma ya ce sai bayan Sallah, haka kuma aka yi. In ba Buhari ba a gaya min wanda Amurka ta taba yi wa haka a duk shugabannin Afirka. Kuma da zuwansa yana cikin abu na farko da ya fara yi na nuna kin amincewa da batun auren jinsi. Ya nuna wa duniya ko shi wane ne. Mutum ne marar tsoro ko fargaba, wanda zai fadi duk abin da yake ganin gaskiya ne.”
Alhaji Idi Zamfare ya ce, kada mutane su manta cewa, ana zargin akwai sa hannun Amurka a batun Boko Haram, “Buhari soja ne wanda har Amurka ya je ya yi karatu, ashe yana da masaniyar wani abu a kanta wanda duk wani kicihin da zasu yi zai iya fahimtar wani abu in ma gaskiya ne akwai hannunta a ciki. Amma muhimmin abu a yanzu shi ne, ko an so ko an ki kowace kasa Amurka na da tasiri a kanta ba wai Najeriya ba, don haka ko ba komai za ta taimaka wa Najeriya wajen kwato kudaden da aka boye a wasu kasashen ba wai a cikinta kawai ba,” inji shi.
Alhaji Idi Zamfare ya ce matsalar Boko Haram da ta addabi Arewa Amurka za ta taka muhimmiyar rawa a wajen yaki da ita domin tun farko ta nemi yin haka a waccan tsohuwar gwamnati, amma saboda rashin hadin kan da ta samu ya sa ta kwashe kayanta ta bar kasar nan. “Tabbacin Amurka za ta taimaka wa Buhari mun ga haka ta irin tarbar da Amurkawa suka yi masa, wadda a tarihi ba mu taba ganin haka ba. Kuma na tabbata, zai kara samo wasu bayanan sirri a kan sha’anin tsaro da wasu batutuwan,” inji Zamfare.
Ya yi kira ga jama’ar Najeriya su ci gaba da yi wa Buhari da kasa addu’ar zaman lafiya da ci gaban kasa. “Na tabbata Buhari da ’yan rakiyarsa sun dawo kasar nan da wasu abubuwan ci gaba ba a fannin kasuwanci da samo karin dabarun tauye barayin kasar nan da masu tayar da zaune-tsaye. Don haka, zuwan Buhari Amurka arziki ne ga Najeriya,” inji shi.