Zuwan Kwankwaso Kano: An nada Dambazau shugaban kwamitin tsaro

A ci gaba da shiryen-shiryen zuwan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Jihar Kano na ranar 30 ga watan Janairu. An kafa kwamitin tsaro karkashin jagorancin Janar Bello Dambazau mai ritaya. Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Dokta Danyaro Ali Yakasai, wanda shi ne mataimakin shugaba da Munir Dahiru a matsayin sakatare. Sai Kanal Garun-Malam mai ritaya, […]

Zuwan Kwankwaso Kano: An nada Dambazau shugaban kwamitin tsaro

A ci gaba da shiryen-shiryen zuwan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Jihar Kano na ranar 30 ga watan Janairu. An kafa kwamitin tsaro karkashin jagorancin Janar Bello Dambazau mai ritaya.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Dokta Danyaro Ali Yakasai, wanda shi ne mataimakin shugaba da Munir Dahiru a matsayin sakatare. Sai Kanal Garun-Malam mai ritaya, da Janar Ahmad Tijjani Jibril mai ritaya, da Air Commodore Salisu Yusha’u mai ritaya, da mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda Bala Abdullahi mai ritaya da sauran manyan hafoshin ‘yan sanda da sojoji masu ritaya.

Daya daga cikin ‘yan kwamitin Alhaji Sunusi Surajo Kwankwaso ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin tabbatar da cewa an gudanar da ziyarar cikin kwanciyar hankali da lumana kuma ya yi alkawarin cewa za su gudanar da taron cikin lumana.