2027: Sardaunan Gombe ya ayyana takarar gwamna a APC
Ya bayyana cewa manufarsa ita ce haɗa kai da jama’a domin bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Gombe, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, wanda aka fi sani da Sardaunan Gombe, ya bayyana aniyarsa a hukumance na tsayawa takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027.
Jamilu, ya mika takardar nuna sha’awarsa tsayawa takarar a ranar Laraba a gundumarsa da ke ƙaramar hukuma.
- Kotu ta soke belin tsohon Shugaban Ma’aikatan El-Rufai
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 5, sun jikkata 2 a Kaduna
Da yake jawabi a sakatariyar APC ta jihar, ya ce kudirinsa na neman kujerar gwamna ya samo asali ne daga burinsa na ganin an ci gaba da gina Jihar Gombe bisa nasarorin da aka samu tare da bullo da sabbin tsare-tsare.
Ya bayyana cewa manufarsa ita ce haɗa kai da jama’a domin bunƙasa tattalin arziki, inganta rayuwar al’umma da kuma tabbatar da shugabanci na gari.
Ya kuma jaddada cewa zai bai wa matasa da mata muhimmanci, tare da inganta ababen more rayuwa cikin tsari mai dorewa.
Ya yi kira ga mambobin APC da daukacin al’ummar Jihar Gombe da su mara masa baya, yana mai cewa lokaci ya yi da za a ƙara ƙaimi wajen gina Gombe.
A nasa ɓangaren, Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Gombe, Mohammed Dantata Ndus, ya yaba masa bisa bin ƙa’idojin jam’iyya, tare da kira ga dukkanin mambobi da su haɗa kai domin samun nasara a zaɓukan da ke tafe.