Kotu ta soke belin tsohon Shugaban Ma’aikatan El-Rufai

A baya an ba da belinsa bayan ya shafe kwanaki 50 a tsare a shekarar da ta gabata.

Kotu ta soke belin tsohon Shugaban Ma’aikatan El-Rufai

Wata kotu a Jihar Kaduna, ta umarci a mayar da Bashir Saidu, tsohon Shugaban Ma’aikatan Tsohon Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai, gidan gyaran hali.

Ana tuhumar Saidu da laifuka da dama, ciki har da zargin rashin gaskiya a harkokin kuɗi.

A baya an ba da belinsa bayan ya shafe kwanaki 50 a tsare a shekarar da ta gabata.

Sai dai a zaman kotu na ranar Laraba, wasu sabbin abubuwa da suka bayyana a shari’ar sun sa kotu ta soke belinsa.

Saboda haka, an sake tsare shi a gidan gyaran hali da ke Kaduna, inda zai ci gaba da zama har sai an ci gaba da shari’arsa a wata mai zuwa.

Wani makusancinsa da ke da masaniya kan lamarin ya tabbatar da soke belin, inda ya ce an soke belin kuma an sake tsare shi.

Saidu, wanda na hannun daman El-Rufai ne, an sake shi a baya, bayan ya cika sharuɗan belinsa, kuma ya ci gaba da harkokin siyasa a Kaduna, musamman a jam’iyyar ADC.