A gudanar da bincike kan kisan fararen hula a Najeriya da Chadi — MDD

Tun daga shekarar 2017 ake samun irin wannan lamari a Arewa maso Gabashin Najeriya musamman a Jihar Borno.

A gudanar da bincike kan kisan fararen hula a Najeriya da Chadi — MDD

Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a gudanar da bincike kan rahotannin kisan gomman fararen hula a wasu hare-hare ta sama da sojojin Najeriya da Chadi suka kai lokuta daban-daban a ƙarshen makon da muka yi bankwana da shi.

Babban jami’in kare haƙƙin bilAdama na MDD, Volker Türk ya ce ya kaɗu da zarge-zargen da ke cewa aƙalla farar hula 100 ne suka mutu a hare-haren da aka kai a wata kasuwa da ke Jihar Zamfara a Arewa maso Gabashin Najeriya da kuma wanda aka kai kan masunta a yankin Tafkin Chadi.

Hukumomin soji dai sun musanta kisan farar hula a samamen da suka kai, inda suka ce an kai hare-haren ne kan masu iƙirarin jihadi kuma an kai su ne bisa tsarin dokokin kare haƙƙin bil adama na ƙasa da ƙasa.

Mai magana da yawun sojojin Najeriya, Manjo Janar Michael Onoja, ya musanta zargin halaka fararen hulan, inda ya ce sun ƙaddamar da farmakin ne kan ’yan ta’adda a yankin kuma suna ci gaba da samun galaba a ƙoƙarinsu na murƙushe ’yan bindiga.

Su ma dai hukumomin Chadi sun ce hare-haren an kai su ne kan mayaƙan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.

Tuni dai Ƙungiyar Amnesty International ita ma ta nemi a gudanar da bincike kan lamarin.

Daraktan ƙungiyar Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sanusi, ya ce bisa bayanan da suka tattara, kusan duka waɗanda abin ya shafa farar hula ne.

Ya ƙara da cewa a makon da ya gabata ma an samu irin wannan lamari a Jihar Neja, inda mutane aƙalla 12 suka rasa ransu — yawancinsu ƙananan yara.

A cewarsa, tun daga shekarar 2017 ake samun irin wannan lamari a Arewa maso Gabashin Najeriya musamman a Jihar Borno, inda a cewarsa, ana kai hare-hare da sunan yaƙi da Boko Haram.