Abin da Ubangiji ya sanar da ni kafin na karbi aikin INEC — Amupitan

Ya kuma shawarci mutane da kada su karɓi wani aiki face sun tabbatar da yardar Ubangiji a cikinsa.

Abin da Ubangiji ya sanar da ni kafin na karbi aikin INEC — Amupitan

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce bai amince ya karɓar aikin hukumar ba sai da ya tabbatar cewa Ubangiji ne ya aminta ya yi aikin.

Yayin da yake magana a Abuja, a wani Taron Baptist na Najeriya da aka shirya, Amupitan ya ce da bai samu karbi aikin ba sai da ya samu tabbaci daga Ubangiji.

Ya ce Ubangiji ya sanar da shi cewa: “Kada ka ji tsoro, kada ka firgita. Zan ƙarfafe ka, zan taimake ka, kuma zan riƙo da kai.”

A cewarsa, wannan saƙo ne da ya ba shi ƙarfin gwiwa tun bayan da ya zama shugaban INEC, musamman wajen fuskantar ƙalubalen gudanar da zaɓe a Najeriya.

Amupitan ya roƙi ’yan Najeriya su ci gaba da yi wa INEC addu’a da kuma nasarar gudanar da zaɓen 2027.

Ya ce yana fatan zaɓen 2027 zai zama mafi kyau a tarihin Najeriya, kuma ya yi imanin hakan zai yiwu da taimakon Ubangiji.

Ya kuma shawarci mutane da kada su karɓi wani aiki face sun tabbatar da yardar Ubangiji a cikinsa.

Shugaba Bola Tinubu ne, ya naɗa Amupitan a watan Oktoban 2025 domin maye gurbin Mahmood Yakubu.

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da yake fuskantar suka kan zargin goyon bayan jam’iyya mai mulki bayan danganta shi da wasu tsofaffin rubuce-rubuce da ya yi kafafen sada zumunta.

’Yan adawa sun nemi ya yi murabus, amma ya musanta mallakar asusun tare da cewa ba shi da alaka da kowace jam’iyyar siyasa.