Alhazan Sakkwato 2 sun rasu a Makkah bayan kammala aikin Hajji

Wasu mata biyu da suka samu hatsari tare da mamatan na ci gaba da karɓar magani a wani asibiti a Saudiyya, inda ɗaya ke jinyar karaya, ɗayar kuma ke fama da targaɗe

Alhazan Sakkwato 2 sun rasu a Makkah bayan kammala aikin Hajji

Wasu alhazan Najeriya a Mina

Wasu alhazai mata biyu daga Jihar Sakkwato sun rasu bayan kammala aikin Hajji a Makkah na ƙasar Saudiyya.

Mataimakin Amirul Hajj kuma Babban Alƙalin Jihar Sakkwato, Alhaji Sodangi Acida, ne ya bayyana cewa alhazan sun gamu da ajalinsu ne a sakamakon hatsari.

Waɗanda suka rasu su haɗa da Hajiya Ladi Umar daga Ƙaramar Hukumar Boɗinga da kuma Hajiya Hadiza Umar daga Ƙaramar Hukumar Yabo.

Acida ya ce wasu alhazai mata biyu da suka samu hatsari tare da mamatan na ci gaba da karɓar magani a wani asibiti a Saudiyya, inda ɗaya ke jinyar karaya, ɗayar kuma ke fama da targaɗe.

Ya isar da ta’aziyyar gwamnatin Jihar Sakkwato ga iyalan mamatan tare da roƙon Allah Ya gafarta musu, Ya kuma sanya su a da Aljannatul Firdaus.

Mataimakin Amirul Hajj ɗin ya ce ana sa ran rukunin farko na alhazan jihar zai tashi daga Saudiyya zuwa Najeriya a ranar 14 ga watan Yuni, yana mai cewa za a gudanar da jigilar dawowar ne bisa tsarin “wanda ya fara zuwa, shi zai fara komawa.”

Ya kuma buƙaci maniyyatan su bi ƙa’idojin kayan da aka amince da su, yana mai jaddada cewa nauyin kayan kowane mahajjaci bai kamata ya wuce kilo 32 ba.