Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato

Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato,

Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato

Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan.

Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje da lalacewar gonaki da rijiyoyi da sauran su.

Mutanen da lamarin ya shafa sun ce suna bukatar agajin gaggawa na abinci da magani da tsaftataccen ruwan sha.

Shugaban karamar hukumar ta Tangaza, Isah Salihu Kalenjeni, ya jagoranci wata tawaga sun ziyarci wuraren da lamarin ya shafa don ganin barnar da ambakiyar ta yi tare da jajanta wa mutanen yankunan.

A yayin ziyarar, Shugaban karamar hukumar ya tabbatar wa mutanen zai sanar da duk wata hukuma da ta dace don kawo masu daukin gaggawa kan halin da suke ciki.

Hukumomi a karamar hukuma da masu bayar da agajin gaggawa sun kuma yi kira wadanda iftila’in ya shafa da su yi aiki tukuru don kare barkewar annobar ciwo ga sauran al’umma.

Aliyu Na Abba daya daga cikin mutanen da ambaliyar ta rusa wa gida da gonaki biyu ya ce yana bukatar hukuma ta tausaya masa halin damuwar da shi da iyalansa suka fada.

Umaima Dan Umaru da ta ke da marayu uku a tare da ita ta ce gonakinsu biyu da suka yi shuka sun lalace sabadiyyar ambaliyar, don haka suna neman agaji.

Ta ce akalla akwai kusan mutum 50 da suka tafka asara a yankin nasu.