Amurka da Iran na zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta
Iran ta jaddada cewa duk wata yarjejeniya ta kawo ƙarshen yaƙin dole ne ta haɗa da dakatar da rikicin da ake yi a Lebanon.
Amurka da Iran sun zargi juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta bayan musayar hare-hare da aka yi a ranar Alhamis, watanni uku bayan fara yaƙin Gabas ta Tsakiya da hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila kan Iran.
Sabbin hare-haren sun kasance mafi muni tun bayan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar a watan Afrilu, lamarin da ya sake kawo cikas a ƙoƙarin da ake yi na kawo ƙarshen yaƙin tare da jawo firgita ƙasar Kuwait, wadda ta zargi Iran da haddasa “mummunar ta’azzara” a yankin.
- Gobara ta kashe ɗalibai 16 a makarantar ’yan mata a Kenya
- Za a cire mutum-mutumin Messi saboda barazanar tsaro a Indiya
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce dakarun ƙasar sun harba makamai kan wasu jiragen ruwa huɗu da suka yi yunƙurin ratsa Mashigar Hormuz ba tare da izini ba, wadda Iran ɗin ta rufe tun bayan ɓarkewar yaƙin a ranar 28 ga watan Fabrairu.
Sojojin Amurka sun ce sun daƙile wasu jirage marasa matuƙa guda biyar a yankin mashigar, sannan suka hana harba wani na shida daga tashar Bandar Abbas da ke kudancin Iran.
Iran ta ce harin da aka kai Bandar Abbas ne ya sa ta kai farmaki kan sansanin sojin Amurka da ta zarga da zama ummul aba’isin harin.
Sai dai Iran ba ta bayyana inda sansanin yake ba, yayin da Kuwait ta ce kariyar sararin samaniyarta ta daƙile wasu makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da suka nufi ƙasarta.
Ma’aikatar harkokin wajen Kuwait ta yi Allah wadai da abin da ta kira “harin takalar faɗa” da Iran ta kai mata, tana mai cewa hakan wani yunƙuri ne na ƙara ruruta rikicin.
Hedikwatar sojojin Amurka ta CENTCOM ta bayyana harin a matsayin “saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta,” yayin da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya ce ƙasarsa za ta ɗauki duk matakan kare martabarta da ikon ƙasarta, tare da zargin Amurka da karya yarjejeniyar.
Wani jami’in Amurka ya shaida wa AFP cewa matakan da suka ɗauka “lissafi ne” kuma an yi su ne domin kare yarjejeniyar tsagaita wuta.
A halin da ake ciki, dakarun juyin juya halin Iran IRGC sun yi barazanar mayar da martani mai tsauri idan aka sake kai musu hare-hare.
Rikicin ya kuma ƙara tsananta a Lebanon, inda Isra’ila ta ayyana yawancin kudancin ƙasar a matsayin filin daga tare da ƙara kai hare-hare har zuwa kusa da Beirut.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kai wani hari a kudancin Beirut, yayin da rundunar sojin Lebanon ta tabbatar da cewa an kai harin ne a wani gini da ke gefen unguwannin kudancin birnin.
Hare-haren Isra’ila a kudancin Lebanon sun kashe aƙalla mutum 14, ciki har da yara uku da wani soja, a cewar hukumomin Lebanon.
Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce adadin waɗanda suka mutu tun bayan fara yaƙin ya kai 3,269.
A gefe guda kuma, sojojin Isra’ila sun ce wani jirgin yaƙin Hezbollah maras matuƙi ya kashe wani sojanta kusa da iyakar Lebanon a ranar Laraba.
Tun bayan fara yaƙin, an kashe sojojin Isra’ila 23 da wani ma’aikacin farar hula guda ɗaya sakamakon hare-haren Hezbollah.
Iran ta jaddada cewa duk wata yarjejeniya ta kawo ƙarshen yaƙin dole ne ta haɗa da dakatar da rikicin da ake yi a Lebanon.