An bindige mutum 5 ’yan gida daya a Filato
’Yan bindiga sun harbe wasu mutum biyar ’yan gida daya a garin Nding da ke Karamar Hukumar Barkin Ladi, Jihar Filato.
‘Yan sanda
’Yan bindiga sun harbe wasu mutum biyar ’yan gida daya a garin Nding da ke Karamar Hukumar Barkin Ladi, Jihar Filato.
Maharan sun kuma bindige wani mutum buda a lokacin harin da suka kai da misalin ƙarfe 9 na dare, ranar Talata.
Harin ya a ƙara firgita mazauna yankin, tare da haifar da damuwa kan yawan maimaituwar hare-haren a sassan jihar.
Wani mazaunin garin mai suna Weng Christopher, ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun shigo yankin suka buɗe wuta kan mutanen.
- ’Yan bindiga sun harbe mutane 24 a Katsina
- ’Yan sanda sun rufe shugabannin ACF a cikin Hedikwatar Ƙungiyar
- Gwamnatin Tinubu tana zubar da ƙimar addinin Islama — Yusuf Baba-Ahmed
A cewarsa, “An kashe mutum biyar ’yan gida daya nan take, yayin da wani mazaunin garin shi ma aka kashe a harin.”
Christopher ya bayyana damuwarsa kan yadda rashin tsaro ke ƙaruwa a yankin, yana mai cewa, “Wannan abu yana yawaita. Kullum a cikin tsoro mutane suke rayuwa.”
Mai magana da yawun ƙungiyar matasan Berom, Rwang Tengwong, ya yi Allah wadai da harin, yana kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki.
Ya ƙara da cewa, ’yan bindiga sun yi ƙoƙarin kai hari a garin Rim da ke Karamar Hukumar Riyom, amma ’yan sa-kai da jami’an Operation Rainbow suka fatattake su.
Tengwong ya bayyana yawan hare-haren a matsayin abin da ya wuce kima, yana kira ga hukumomi da su ƙara ƙoƙari wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Plateau.
Hukumomin tsaro ba su yi wani bayani kan lamarin ba har zuwa lokacin da aka kammala rahoton.