An cafke mutun 6 kan lalata kananan yara a Kebbi
Wasu mutum shida da ake zargi da lalata kananan yara sun shiga hannun jami’an tsaro a Jihar Kebbi.
Wasu mutum shida da ake zargi da lalata kananan yara sun shiga hannun jami’an tsaro a Jihar Kebbi.
Kwamshinan ’yan sandan jihar, Samuel Musa, ya ce jami’an rundunar sun kama mutanen ne bayan an gano biyar daga cikinsu sun yi lalata da wata karamar yarinya a Karamar Hukumar Koko-Besse.
Bayan haka, wani magidanci daga garin Aliero ya kawo kara cewa daya daga cikin wadanda ake zargin ya i wa ’yarsa mai shekara 10 fyade, sannan ya yi mata barazanar kisa idan ta fada wa wani.
Ya kara da cewa ‘Wani magidanci a Karamar Hukumar Koko-Besse ya kawo mana kara cewa ’yarsa mai shekara 16 ta bar gida ba a san inda take ba.
“A yayin bincike jami’anmu suka gano ta a garin Koko inda ta shaida musu cewa mutum biyar daga cikin wadanda ake zargin sun yi lalata da ita.
“Sun rika yaudararsu ne zuwa gidajensu a lokuta daban-daban suna yin lalata da ita, amma yanzu suna hannun za a gurfanar da su a gaban kuliya.
“A ranar 24 ga watan Juli kuma jami’anmu sun kama wata mata daga kauyen Babbar Dogo na Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara dauke da harsasai guda 566,’’ in ji kwamishinan ’yan sandan.
Jami’an sun kamu kwace bindigar harba roka guda daya bayan sun ragargaji gungun wasu ’yan bindiga da suka kai hari kauyen Dan-umaru da ke Karamar Hukuamr Danko/Wasagu, inda maharan suka tsere da raunukan harbi.