An ci zarafin yara 205 a Gombe a wata 10
Alƙaluman na nuni da yadda matsalar ke ƙara kamari a jihar, musamman a tsakanin yara, tare da buƙatar ƙara ƙaimi wajen daƙile ta
Aƙalla mutum 205 ne aka ci zarafinsu ta hanyar jima’i ko na jinsi a Jihar Gombe tsakanin watan Mayu 2025 zuwa Maris 2026, inda yara da matasa suka fi fuskantar wannan matsala.
Bayanan sun fito ne daga Cibiyar Taimakon Wadanda Aka Yi wa Fyaɗe (SAC) da ke Asibitin Kwararru na Jihar Gombe.
Jami’ar da ke kula da cibiyar, Balkisu Ali, ce ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki kan kare haƙƙin yara da Ofishin UNICEF na Bauchi ya shirya. Taron ya haɗa mahalarta daga jihohin Adamawa, Bauchi da Gombe.
Alƙaluman sun nuna cewa mata ne suka fi yawa a cikin waɗanda abin ya shafa da mutum 152, yayin da maza suka kai 43.
- Abba ya zaɓi Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano
- DAGA LARABA: Shin kare kai daga harin ’yan ta’adda zai kawo karshen matsalar tsaro?
Dangane da shekaru, yara masu shekaru 10 zuwa 14 sun fi yawa da mutum 51, sai masu shekaru 15 zuwa 19 da suka kai 43.
Haka kuma, yara masu shekaru biyar zuwa tara sun kai 41, yayin da ƙananan yara ’yan ƙasa da shekara guda zuwa shekara hudu suka kai 12.
A ɓangaren manya kuwa, an samu mutum 19 masu shekaru 20 zuwa 24, yayin da 39 ke da shekaru 25 zuwa sama.
A faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar, Karamar Hukumar Gombe ce ta fi yawan alƙaluma da 112, sai Akko da ke da 74.
Sauran ƙananan hukumomi sun samu rahotanni kaɗan, yayin da Funakaye da Shongom ba su samu ko guda ba.
Daga cikin dukkan rahotannin, guda 166 na cin zarafin jima’i ne, yayin da 39 suka shafi cin zarafi a cikin gida.
Duk da yawan alƙaluman, shari’o’i shida kacal aka kai gaban kotu zuwa yanzu, lamarin da ke nuna ƙalubale wajen hukunta masu laifi da samar da adalci ga waɗanda aka ci zarafi.
Sai dai an samu wasu matakan taimako, inda mutum 40 suka samu taimakon shari’a, yayin da aka tura shari’o’i 101 domin ƙarin tallafi.
Alƙaluman na nuni da yadda matsalar ke ƙara kamari a jihar, musamman a tsakanin yara, tare da buƙatar ƙara ƙaimi wajen daƙile ta ta hanyar wayar da kai da kuma tsaurara matakan doka.