An ga watan Ramadan a Najeriya

Sarkin Musulmin ya amince da rahotannin ganin watan da aka samu daga wurare daban-daban a sassan Nijeriya.

An ga watan Ramadan a Najeriya

Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya sanar da ganin watan Ramadan na shekarar 1447 Hijiriyya a yau Talata, 29 ga Sha’aban, wanda ya yi daidai da 17 ga watan Fabrairu, 2026.

Sarkin Musulmin ya amince da rahotannin ganin watan da aka samu daga wurare daban-daban a sassan Nijeriya, bayan tantance su kamar yadda aka saba.

A wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanya wa hannu, an bayyana cewa Sarkin Musulmin ya ayyana gobe Laraba a matsayin 1 ga watan Ramadan 1447AH.

Sarkin Musulmin ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rungumi watan azumi da tsoron Allah, tare da ƙara himma wajen ibada da ayyukan alheri.

Haka kuma ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya sanya albarka a cikin watan, Ya kuma bai wa ƙasa zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.

Sanarwar ta ce ya dace al’umma su yi amfani da wannan wata mai alfarma wajen yi wa Nijeriya addu’ar zaman lafiya da warware matsalolin da ake fuskanta.