An kafa dokar hana zance tsakanin saurayi da budurwa a Kano
Al’ummar yankin sun kafa dokokin ne domin tsarkake tarbiyyar matasa da kuma inganta tsaro.
Al’ummar unguwar Sharada da ke Ƙaramar Hukumar Birni a Jihar Kano, sun ƙirƙiro dokoki 29 domin gyara halayyar jama’a da kare lafiyar mutane da dukiyoyinsu.
Daga cikin dokokin akwai hana saurayi da budurwa yin zancen dare, musamman a cikin mota, da kuma hana su wuce ƙarfe 10 na dare suna hira a waje.
- Ba mu da tabbas na ci gaba da rijistar kaɗa ƙuri’a a Borno — INEC
- Mutum 12 sun rasu, 5 sun jikkata a hatsarin mota a Kano
Mahukuntan yankin sun ce sun ɗauki wannan mataki ne saboda damuwa kan lalacewar tarbiyya, ƙaruwa matsalolin tsaro, da kuma rashin bin al’adun da suka dace musamman a tsakanin matasa.
Wannan ba shi ne karon farko da aka taɓa kafa irin wannan doka ba a jihar.
A baya, unguwanni irin su Fagge, Tudun Yola, Kurna da sauransu sun taɓa kafa irin wannan doka, domin kula da tarbiyyar matasa.