An kama wasu mutane da ake zargi da fashi a Legas
Majiyoyin ’yan sanda sun bayyana cewa, waɗanda ake zargin sun daɗe suna tsoratar da mazauna yankin tare da ƙwace musu kayayyakinsu kafin cafke su.
Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Legas sun kama mutane uku da ake zargi da fashi a yankin Idimu da ke Legas, inda suka ƙwato babur ƙirar Bajaj da wasu kayayyakin laifi yayin gudanar da aikin.
An kama waɗanda ake zargin ne biyo bayan wani samame da jami’an ’yan sanda suka kai sakamakon bayanan sirri da suka samu kan ayyukan wani rukunin ’yan fashi da ke addabar yankin Idimu.
An bayyana sunayen mutane ukun da aka kama kamar haka: Abdullahi Mustapha (mai shekara 20), Salisu Sannusi (mai shekara 30), da kuma Jamiu Sahidu (mai shekara 26).
Majiyoyin ’yan sanda sun bayyana cewa, waɗanda ake zargin sun daɗe suna tsoratar da mazauna yankin tare da ƙwace musu kayayyakinsu kafin cafke su.
Abubuwan da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da babur ƙirar Bajaj wanda ake kyautata zaton na sata ne, da ma wasu kayayyaki da ke da nasaba da ayyukansu na laifi.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Legas, SP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da kama su, inda ta ce hakan na cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi na daƙile ayyukan laifi a faɗin jihar.
“A daren ranar Talata, 7 ga watan Afrilu, 2026, da misalin ƙarfe 2:00 na safe, jami’an rundunar da ke sintiri a shiyyar Car Wash Bus-Stop kusa da First Bank, a yankin Idimu, sun tsayar da wasu mutane uku a kan babur.
“Binciken da aka gudanar a kansu ya kai ga gano adda da aka ɓoye a cikin tufafinsu, kayan sojoji, wayoyin salula huɗu, power bank guda ɗaya, waɗanda ake zargin sun ƙwace su ne daga hannun masu su, wasu takardun kuɗi na Naira, da kuma babur ƙirar Bajaj mai lamba AKD 40 OM, wanda ake amfani da shi wajen zirga-zirga don ƙaddamar da ayyukan fashi.
“Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun ƙware wajen yi wa jama’a fashi kafin su tsere daga wurin.