Mutum 8 sun mutu a sabon hari a Filato
Yayin da yake tabbatar da harin na Vole, Shugaban Majalisar Matasa ta Jihar Filato (PYC) reshen Bokkos, Dakol James ya ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 8:00 zuwa 9:00 na dare.
Aƙalla mutane takwas ne aka bayyana cewa an kashe, yayin da wasu huɗu suka ji rauni a daren ranar Alhamis, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari a yankin Vole da ke Gundumar Kwatas, a Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato.
Wannan sabon hari ya faru ne kwana guda bayan wasu makamantan hare-hare da aka kai a wani wurin haƙar ma’adinai a ƙauyen Kok da ke gundumar Ropp da kuma ƙauyen Chenye da ke gundumar Bachi a ƙananan hukumomin Barkin Ladi da Riyom, inda aka kashe mutane biyu.
Yayin da yake tabbatar da harin na Vole, Shugaban Majalisar Matasa ta Jihar Filato (PYC) reshen Bokkos, Dakol James ya ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 8:00 zuwa 9:00 na dare.
Yayin da yake Allah-wadai da harin, ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa don kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan.
“ɗaukacin matasan Bokkos suna matuƙar takaici da yanayin tsaro. Har zuwa safiyar yau, babu jami’an tsaro ko ɗaya da aka tura don duba halin da ake ciki. An kwashe kusan sa’o’i 12, amma ba mu ga wani jami’in tsaro ba,” in ji shi.
Haka kuma, wani jagoran matasa a Bokkos, Christopher Luka ya bayyana cewa ya fara jin ƙarar harbe-harbe ne tun misalin ƙarfe 8:00 na dare, amma bai gano daga inda suke fitowa ba a lokacin.
“Lokacin da na ji ƙarar harbin, na fara kiran wasu don jin inda harbin yake fitowa. Kafin wannan lokacin, yankin yana cikin kwanciyar hankali.
“Ba a samu wani tashin hankali ba kwanan nan, don haka wannan harin ya zo mana a matsayin abin mamaki. Muna Allah-wadai da harin da kuma rashin jami’an tsaro a wurin,” in ji shi.
Luka ya ƙara da cewa, shugabannin matasa sun yi ta ƙoƙarin kwantar wa mazauna yankin hankali, tare da yin kiran da a bi komai cikin natsuwa yayin da ake jiran martani daga jami’an tsaro. “Sun amince da kiranmu na kwantar da hankali,” in ji shi.
Haka zalika, Shugaban Ƙungiyar Fulani ta Gan Allah (GAFDAN) a Bokkos, Saleh Adamu, ya yi Allah-wadai da harin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici kuma mara dalili.