An kamo babban jami’in Binance da ya tsere daga Najeriya a Kenya
A wannan mako ake sa ran taso keyar Nadeem Anjarwalla zuwa Najeriya daga Kenya
Jami’an tsaron kasa da kasa (Interpol) sun kama babban jami’in kamfanin crypto na Binance, Nadeem Anjarwalla, wanda ya tsere daga hannun gwamnatin Najeriya.
Interpol sun kama Nadeeem Anjarwalla ne a kasar Kenya, inda suke shirye-shiryen taso keyarsa zuwa Najeriya domin fuskantar shari’a.
Jaridar Punch ta ruwaito wasu jami’an gwamanti na tabbatar da kama Nadeem a kasar Kenya, da kuma cewa a cikin makon nan Interpol za su kawo shi Najeriya.
Nadeem Anjarwalla ya tsere daga hannun hukumomin tsaron Najeriya ne a yayin da yake fuskantar shari’a kan ayyukan kamfaninsa da gwamnatin kasar ta haramta, kan alaƙar Binance da Badakala Tashin Dala.
Kamfani Binance da Najarwalla da wani babban daraktan kamfanin mai suna Tigran Gambaryan da ke tsare a hannun EFCC na fuskantar zargin kin biyan haraji, safarar kudaden haram Dala miliyan 35.4 da kuma kawo rudani a kasuwar canjin kudaden kasashen waje a Najeriya, wanda ya yi sanadin tashin gwauron zabon Dala da kuma ƙaruwar darajar Naira.
Kafin yanzu rahotanni sun nuna cewa an gano motsin Nadeem a Kenya, bayan tserewarsa daga Najeriya, kuma gwamnati na aiki da hukumomin Kenya domin kamo shi domin ya girbi abin da ya shuka.
Daga bisani ne hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arziki da hukumar ’yan sandan Kenya da ma Interpol suka zurfafa bincike, daga karshen ’yan sanda suka kamo shi a Kenya.